Nijeriya a 64: Shugaban NATA ya buƙaci shugabanni su ɗauki muhimman matakai don rage tsananin rayuwa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙungiyar Masu Fasahar Gyaran Ababe Hawa na ƙasa, NATA, Ambasada Injiniya Dakta Magaji Muhammad Sani ya shawarci shugabannin ƙasar nan da su ɗauki muhimman  matakai domin rage wahalhalun da ‘yan ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da yan jarida gameda cikar kasarnan shekaru  64 da samun yancinta .

Ya ƙara da cewa duk irin wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a yau su ƙudure ba su da wata ƙasa da ta fi Nijeriya su cigaba da nuna kishi.

Ambasada Dakta Magaji Muhammad Sani ya ce dole ne shugabanninmu musamman ’yan siyasa su sani cewa jama’ar ƙasar nan ne suka zaɓe su domin su yi musu hidima.

Ya ƙara da cewa shugabanni a ƙasar su yi kyakkyawan tunani na  ɗaukar manyan matakai da za su kai mutane zuwa ingantacciyar rayuwa ba tare da wahala ba.

Sannan sai ya yi  addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya baiwa shuwagabannin mu kyakkyawan tunani a kan abin da ya kamata su yi domin su jagoranci al’umma ta hanyoyi nagari.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da kowa ya ji tsoron Allah ya tsaya a kan gaskiya a kodayaushe su kuma yi addu’ar Allah ya shiryar da shugabannin mu.

Injiniya Ambasada Injiniya Dakta Magaji Muhammad Sani  ya yi kira ga ‘yan ƙungiyarsu ta  NATA  su ƙara ƙaimi da ƙara yin haƙuri kuma su ƙara himma da riƙe gaskiya a aikinsu kuma su ƙudure cewa halin ƙuncin da muke ciki wani abu ne da ya zo kuma zai wuce da yardar Allah.

By ukarofi