Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya (NFF) ta bayyana cewa, tawagar ’yan wasan ƙasarta na Super Eagles za su fafata da takwarorinsu na Ƙasar Ghana a wasan neman tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da Ƙasar Ƙatar za ta karɓi baƙunci a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abuja.
Sanarwar ta NFF ta ce, za a yi wannan karawar ne a ranar 27 ga watan Maris.
A halin yanzu a na dakon sanarwa daga Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ghana kan zagayen farko na wasan neman cancantar da za su buga, wanda ake sa ran ya gudana ko dai a ranar 23 ga watan na Maris ko kuma a ranar 24 ga watan.
Baya ga wasan Nijeriya da Ghana, Jaddawalin wasannin neman tikitin halartar Gasar Cin Kofin Duniya da za ta gudana a Ƙatar ya nuna cewa, Masar da Senegal za su sake kece raini a cikin watan Maris, inda kowacce ƙasa za ta yi tattaki zuwa gidan abokiyar hamayyarta.
A sauran wasannin neman tikitin zuwa Gasar ta Cin Kofin Duniya a Ƙatar, Ƙasar Kamaru za ta kara da Ƙasar Aljeriya, sai Mali da Tunisia, sai kuma Jamhuriyar Dimukaraɗiyyar Kongo da za ta fafata da Moroko.