Fafaroma Benedict ya roƙi yafiyar lalata yaran da limaman Katolika suka yi

Tsohon Shugaban mabiya ɗariƙar Katolika na duniya Fafaroma Benedict na 16, ya nemi gafarar jama’a, kan samun wasu limaman Cocin da cin zarafin yara lokacin jagorancin sa a Ƙasar Jamus.

A wasiƙar da ya rubuta dangane da zargin cin zarafin yaran da ake bincike a Ƙasar Jamus lokacin da yake jagorancin mujami’ar Katolika da ke birnin Munich, Benedict na 16 ya ce, babu abinda zai shaida wa waɗanda aka ci zarafin su sai baƙin cikinsa da kuma kunya tare da buƙatar su yafe masa.

Tsohon Fafaroman ya ce, ya samu dama sosai wajen jagoranci a Cocin Katolika, kuma ɗaukacin nauyin cin zarafi da kuskuren da aka samu sun rataya ne akan sa.

Benedict na 16 ya sauka daga muƙaminsa a shekarar 2013, yayin da aka zarge shi da ƙin dakatar da wasu fada fada guda 4 da ake zargin su da cin zarafin yara ƙanana a shekarar 1980 lokacin da ya jagoranci mujami’ar da ke Munich.

Tsohon Fafaroman da ke fama da rashin lafiya, saboda yawan shekarunsa, ya buƙaci masu taimaka masa da su taimaka masa wajen amsa tambayoyin da aka masa daga Cibiyar lauyoyin Westpfahl Spilker Wasti wanda mujami’ar Munich da ta Freising suka ɗora wa alhakin gudanar da bincike akan cin zarafin da aka samu daga shekarar 1945 zuwa 2019.

Masu taimaka wa Benedict na 16 sun haƙiƙance kan cewar, bai aikata wani laifi wajen rufa-rufa dangane da zargin cin zarafin ba.

Tsohon Fafaroman wanda aka fi sani da Joseph Ratzinger kafin naɗa shi shugaban mabiya ɗariƙar Katolika na duniya, ya jagoranci mujami’ar Munich daga shekarar 1977 zuwa 1982.