Nijeriya na iya zaɓen tikitin Kirista-Kirista – Gwamna Sule

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa, yana da yaƙinin cewa, wata rana Nijeriya za ta zaɓi shugaban ƙasa da mataimakinsa, waɗanda dukkansu Kiristoci ne, duk da ci gaba da muhawarar da ta biyo bayan matakin Jam’iyyar APC na ci gaba da tsayar da tikitin Musulmi-Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talbijin na Channels, Sule ya ce Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 bai tanadi wajabcin daidaita addini a tikitin takarar shugaban ƙasa ba, yana mai jaddada cewa ƙwarewa da kuma bin ƙa’idar Federal Character ne ya kamata su kasance abin la’akari.

Kalaman gwamnan na zuwa ne bayan da APC ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nemi wa’adi na biyu tare da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, abin da ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin cewa jam’iyyar na iya maye gurbin Shettima da wani Kirista daga Arewa.

Da aka tambaye shi game da sukar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kan tikitin Musulmi-Musulmi, Gwamna Sule ya ce hakan ba abin mamaki ba ne, domin yana cikin jam’iyyar adawa.

Ya ce yana mutunta Kwankwaso, amma a matsayinsa na ɗan adawa ba za a yi tsammanin zai yaba wa APC ba. Gwamnan ya nace cewa babu inda Kundin Tsarin Mulki ya wajabta a yi la’akari da addini wajen zaɓen shugaban ƙasa ko mataimakinsa. A cewarsa, sashe na 14 da na 15 na Kundin Tsarin Mulki sun fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa da tsarin Federal Character, ba wai raba muƙamai bisa addini ba.

Sule ya yi nuni da nasarar marigayi MKO Abiola da Babagana Kingibe a zaɓen 1993, da kuma nasarar Tinubu da Shettima a zaɓen 2023, a matsayin hujjar cewa tikitin ’yan takara masu addini ɗaya na iya samun karɓuwa daga masu zaɓe.

Ya ce: “Ina addu’ar wata rana Nijeriya ta samu tikitin Kirista-Kirista, kuma ya yi nasara. Wannan shi ne abin da nake fatan gani.”

Gwamna Sule ya ce gwamnatinsa ta nuna cewa addini ba shi ne ma’aunin ba da mukami ba, domin tun lokacin da ya hau mulki yake aiki tare da mataimakinsa, Emmanuel Akabe, wanda Kirista ne. Ya ce zaɓensa ya samo asali ne daga ƙwarewa da cancanta, yana mai ƙara da cewa yanayin siyasa a Nasarawa ya bambanta da na ƙasa baki ɗaya. Haka kuma ya ce wasu jihohi irin su Enugu da Bayelsa sun daɗe suna da shugabanci na Kirista-Kirista ba tare da wata muhawara ba. Rahoton ya ce batun ya sake ɗaukar zafi ne bayan APC ta tabbatar da ci gaba da tikitin Tinubu da Shettima a 2027.

Masu sukar wannan tsari sun yi zargin cewa yana tauye daidaiton addinai a ƙasar, sai dai duk da hakan, Tinubu da Shettima sun yi nasarar lashe zaɓen 2023, lamarin da ya sa jam’iyyar ta ci gaba da wannan haɗin gwiwa.

Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa a yanzu hankalin ƙasashen duniya ya fi karkata kan batun tikitin Musulmi-Musulmi fiye da batutuwan da ake ta cece-kuce a kansa.

Sai dai wasu jam’iyyun siyasa sun ce ƙwarewa ce ya kamata ta kasance ginshiƙin zaɓe.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APGA, Ejimofor Opara, ya ce abin da ya kamata ’yan Nijeriya su duba shi ne cancanta da iya shugabanci, ba addinin ɗan takara ba.

Haka shi ma kakakin Jam’iyyar YPP, Wale Egbeola Martins, ya bayyana cewa babbar matsalar Nijeriya ita ce rashin nagartaccen shugabanci, ba addinin masu mulki ba.

A nata ɓangaren, APC ta kare matakin ci gaba da tikitin Musulmi-Musulmi, tana mai cewa an yanke shawarar ne bayan nazari mai zurfi da kuma la’akari da muradun ƙasa baki ɗaya.

Masana harkokin siyasa kuwa na ganin cewa muhawarar addini a tikitin shugaban ƙasa za ta ci gaba da ɗaukar hankali kafin zaɓen 2027, duk da cewa batutuwan tsaro, tattalin arziki da ingancin shugabanci na iya zama manyan abubuwan da za su rinjayi zaɓin ’yan Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply