Nijeriya ta jajenta wa Jamus kan mutuwar tsohon shugabanta

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta miƙa ta’aziyyarta ga gwamnatin da al’ummar Jamus bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Horst Köhler, wanda ya rasu a ranar 1 ga Fabrairu yana da shekaru 81. Köhler ya yi mulki daga 2004 zuwa 2010, kuma an san shi da ƙoƙarinsa wajen ƙarfafa alaƙar Jamus da Afirka, musamman a fannin ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a Abuja, ya bayyana rasuwar Köhler a matsayin babban rashi ga duniya. Ya ce tsohon shugaban ya kasance jajirtacce wajen inganta haɗin kan ƙasashen duniya, ci gaban tattalin arziki, da samar da dawwamammen zaman lafiya a duniya baki ɗaya.

Tuggar ya jaddada cewa Köhler ya taka rawar gani wajen kyautata dangantakar Jamus da ƙasashen Afirka, ciki har da Najeriya, inda ya ƙaddamar da shirye-shirye da dama don samar da zaman lafiya, bunƙasa tattalin arziki, da fahimtar juna tsakanin nahiyoyin biyu. Ya ce jajircewarsa wajen samar da duniya mafi kyau za ta cigaba da zama abin koyi ga manyan shugabanni masu zuwa.

A ƙarshe, ministan ya ce Najeriya tana tare da al’ummar Jamus a wannan lokaci na jimami, tare da girmama kyakkyawan tarihin tsohon shugaban. Ya kuma yaba da rawar da Köhler ya taka wajen yaƙi da fatara da kuma ƙirƙiro shirin haɗin gwiwa tsakanin Afirka da Turai domin inganta hulɗa da cigaba mai ɗorewa.

By ukarofi