
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar ƴan jarida ta Ƙasa, NUJ ta yi alla-wadai da cin mutunci da wulaƙanta ƴan jaridan da ke ɗaukar rahotannin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya da wasu ke yi.
Sakataren ƙungiyar, Achike Chude ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi inda ya ce duk da ƙalubalen da ƴan jarida ke fuskanta, hakan bai sanya su kasa sauke nauyinsu na sanar da al’umma, wayar mu su da kai da kuma ilimantar da su ba.
Ya ce, ƴan jarida sun yi ta ƙoƙarin ruwaito labarai kan yadda ta ke kasancewa a zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya wanda a yayin hakan su ke haɗuwa da matsalolin cin mutunci da wulaƙanci inda har ta kai ga ƙwace mu su kayayyakin aiki da ma na amfanin kansu.
A jihar Legas, ƴan sanda da jami’an LCC sun hana ɗan jarida Bernard Akede na gidan telebijin ɗin News Central yin hira ta kai-tsaye.
A Calabar, babban birnin Jihar Cross-River kuwa, wasu ɓata-gari ne su ka farmaki ƴan jarida inda wani wakilin jaridar ‘Nigerian Tribune’, Joseph Abasi-Abasi ya samu mummunan rauni da kuma harin wata motar abinci da ta nufin gidan ‘Etim Ernest Press Center’.
Haka nan a Abuja, an kama ɗan jaridar ɗaukar hoto na ‘Daily Independent’ ba bisa ƙa’ida ba sannan ƴan sandan su ka ƙwace wayar salularsa. Bayan da wasu ƴan jarida su ka yi zanga-zanga ne, sai aka sako shi.
Sauran gidajen jaridun da lamarin ya shafa sun haɗa da; The PUNCH, Premium Times, Cross-River Watch da Radio Ndarason Internationale.
NUJ ta buƙaci a yi bincike kan al’amurran domin a hukunta waɗanda ke da hannu a cikin wulaƙanta ƴan jaridan. Haka ma su na neman hukumomin da abin ya shafa, su aiko da saƙon bada haƙuri da kuma biyan ababen da aka lalata.
