
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Pafaroma Leo na 14 (XIV), ya yi watsi da ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a taɓarɓarewar harkokin tsaron Nijeriya, inda ya ce al’amarin ya shafi Kiristoci, Musulmai da yankuna da dama na ƙasar.
Jagoran addinin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da ya ke ganawa da ƴan jarida da yake barin gidansa na Castel Gandolfo da ke Vatican a ƙasar Italiya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi amsa tambaya game da halin tsaron da al’ummar Kiristocin Nijeriya ke ciki, yana mai cewa al’amarin ta’addanci a ƙasar na faruwa ne saboda dalilai na matsin tattali, rikicin karɓe iko da yanki da albarkatun ƙasa ba wai ƙoƙarin shafe Kiristoci ba.
Ya kuma ce, halin ya wuce batun addini domin abu ne da ya yi sanda rasa rayukan da dama daga mabanbanta addinai a sassan ƙasar.
Hakan zuwa ne makonni kaɗan da Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta (CPC) sakamakon abinda ya kira da tauye ƴancin al’ummar Kiristoci wajen yi musu kisan kiyashi a ƙasar.
Tuni dai gwamnatin Nijeriyar ta masunta zargin inda ta ce hakan gurguwar fahimta ce da aka yi wa halin rashin tsaro a ƙasar, wanda ya shafi ɓangarorin Kirista da Musulmi.
