
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya gaggauta ƙaura zuwa Jihar Kebbi domin jagorantar yadda za a ceto ɗalibai ƴan mata guda 25 da aka yi garkuwa da su a farkon wannan makon.
A safiyar ranar Litinin ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan bindiga sun kutsa makarantar mata ta Government Girls’ Secondary School, Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu na jihar da misalin ƙarfe 4, inda suka yi awon-gaba da ɗaliban.
Tinubu ya bayar da umarnin ne ta bakin Kakakinsa Bayo Onanuga a ranar Alhamis.
Ya ce, Ministan zai cigaba da zama a Kebbi sai lokacin da aka kammala dukkan ayyukan yunƙurin sako ƴan matan. A yau Juma’a ake sa ran Matawalle zai isa Birnin Kebbi.
Ana ganin hakan a matsayin wata hanya ta nuna ƙwarewar ministan wajen kula da lamuran da suka ayyukan ƴan bindiga da garkuwa da ɗalibai musamman wanda ya samu a Jiharsa ta Zamfara daga 2019 zuwa 2023 a lokacin da ya ke gwamna.
Daya daga cikin ayyukan ta’addancin shi ne a ranar 26 ga Fabarairun 2021, lokacin da ƴan bindiga suka yi awon-gaba da ɗalibai mata 279 na makarantar Government Girls Science Secondary School, Jangebe. Daga bisani aka sako su a ranar 2 ga watan Maris, 2021.
Rahotanni daga hukumomin tsaro ga Shugaba Tinubu a kullum ya sa ya jinkirta tafiyarsa ta ziyarar aiki a Afirka ta Kudu da Angola domin ganin an shawo kan al’amuran.
Fadar Shugaban Ƙasa ta jaddada ƙudirinta na tabbatar da an ceto ɗaliban da masu ibada su 38 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara, inda tuni aka fara aikin farauto masu hannu a laifin.
