RA’AYI: Me ya sa za mu munana wa Allah zato?

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Talakawa ne kawai suke yin saɓo da su kaɗai Allah zai jarabta da yunwa da fatara da talauci, ya bar shugabanni su na yin wadaƙa da kuɗi, su ba zai jarabce su be?

Wallahil azim, ba Fauziyya D. Sulaiman kaɗai ba, ni kaina kusan kullum sai an kira ni a waya ana neman taimako waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba. Ban da mutane na zahiri da za su tare ka gaba da gaba su ce suna neman taimako, banda masu sakon ‘teɗt massages, banda masu bugo waya, banda masu zuwa gida. Wallahil azim abin har tsoro yake ba ni.

Duk kuɗin ka da ka ajiye, idan ka fito da su ka ce raba wa masu neman taimakon za ka yi, kai ma za ka dawo ka bi layi ne cikinsu.

Ya Allah ka warware mana waɗannan matsalolin. Ka kawo wa kowa yadda zai yi. Wallahil azim Ina rubutun nan akwai magidancin da ya kira ni a waya ya katse min rubutun wai yana neman taimako, babu abinda zai ci a gidansa.

Masu mulki ne suka jefa talaka cikin wannan masifar, ba Allah ba ne. Mu daina munana wa Allah zato. Allah yana son mu, yana son bayinsa. Akwai ƙasashen da babu Musulmi guda dubu goma a ƙasar. Kai Babu ma Musulmi dubu ɗaya a ƙasar, irinsu Italy da Agentina kuma suna auren jinsi, amma talakawansu suna rayuwa cikin jin daɗi da walwala.

Ni masu ba ni haushi su ne masu cewa, wai zunubanmu ne. Me ya sa su masu mulkin zunubansu bai sa sun jarabta da fatara da yunwa da talaucin ba? Ba su fi talaka yin saɓo ba? Su ne mashaya giya, su ne masu yin zina da luwaɗi, su ne masu kisan kai, su ne masu cin naman mutane, su ne masu yin auren jinsi, su ne masu neman jininsu da zina ko wata nau’in lalatar, amma duk su Allah da yake yana son su, bai jarabce su ba? Sai Talaka da ba ya ‘so’ zai jarabta? Wannan munanawa Allah zato ne!!!

Allah ya kawo wa talakan Nijeriya sauƙi da kuma shugabanni nagari.

Laraba, 23 ga August, 2023

Abdullahi Jibril Larabi, wanda ake yi wa laƙabi da Uncle Larabi, marubuci ne kuma manazarci a Kano

By ukarofi