Nijeriya za ta samu ƙarin kuɗaɗe bayan tashin farashin ɗanyen mai a duniya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Akwai yiwuwar gwamnatin Nijeriya ta samu ƙaruwar kuɗaɗe a ɓangaren kasuwar ɗanyen mai biyo bayan tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.

An ce, hakan ya sa farashin man fetur ya tashi a duniya.

An fara kasuwancin ɗanyen mai a wannan makon tare da samun riba, bayan da aka shafe wani mako na asara, yayin da ƙaruwar tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya ya haifar da damuwa.

ɗanyen mai na Brent yana a kan sama da dala 79 a kasuwanin yammacin Asiya a yau, tare da Teɗas Intermediate sama da dala 75 a kan kowace ganga.

Idan dai ba a manta ba, Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya (NBS) ta sanar cewar yawan ɗanyen mai da ƙasar ke haƙowa a kullum ya ragu da gangan 160,000.

NBS ta bayyana cewa adadin ɗanyen man da Nijeriya ke haƙowa domin fitarwa kasuwannin duniya ya ragu zuwa ganga miliyan 1.41 daga ganga miliyan 1.57.

Ta bayyana cewa an samu raguwar haƙo ɗanyen man ne a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Yuni na shekarar 2024 muke ciki.

Sai dai ta bayyana cewa duk da haka, yawan kayan da ake samarwa a Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.19 a cikin 100.

By ukarofi