Gwamnatin Yobe ta ƙudiri aniyar bada filin jirgin samanta ga masu zuba jari

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa a gwamnatin jihar za ta ba da filaye kyauta tare da wasu abubuwan ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari masu son zuba jari a babban filin jirgin saman Damaturu.

Gwamnan ya ce, bayan kammala titin jirginsa mai tsawon kilomita 3.6, ginin tasha da kuma shimfiɗa na’urorin jiragen sama da kuma tsarin da yake da shi, filin jirgin zai shirya tsaf don fara kasuwanci.

Buni ya yi magana ne a taron kasuwanci na filin jirgin sama na 2024 da aka yi a Legas inda ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta baiwa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) umarnin haɗa kai da gwamnatin jihar Yobe wajen ganin an buɗe filin jirgin domin gudanar da ayyuka masu inganci musamman na haɓaka kayan amfanin gona.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban sakatare na ma’aikatar sufuri da makamashi ta jihar Yobe, Dr. Mustapha Gaidam, ya tabbatar da cewa jihar ta fi kowacce yawan noma da dabbobi a faɗin ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa filin jirgin zai fi zama wurin zirga-zirgar ababen hawa a ƙasashen da ke makwabtaka da su, idan ana fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje yayin da suke samar da maƙudan kuɗaɗen shiga ga jihar Yobe da gwamnatin tarayya.

By ukarofi