Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawa ta bakin kwamitinta kan bin doka da oda, ta sha alwashin sanyawa takunkumi kan duk wani shugaban hukumar Gwamnatin Tarayya da aka tuhuma da laifin zamba a cikin rahoton da ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasa (OAuGF) ya mika wa majalisar.
Shugaban kwamitin Sanata Garba Madoki ne ya yi wannan gargaɗin a ranar Litinin a Abuja a wajen wani taron bita na yini ɗaya kan ‘ƙarfafa bin doka da oda don gudanar da ingantaccen shugabanci.
Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuraɗiyya ta ƙasa (NILDS) tare da haɗin gwiwar Konrad Adenauer Stiftung (KAS) ne suka shirya taron bitar ga mambobin kwamitin.
Odita-Janar a ’yan watannin baya, ya yi tsokaci kan ɓacewar zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 105.66 a ɓangaren ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Odita-Janar ya yi nuni da cewa, ba za a iya fuskantar gaskiya da riƙon amana a tsarin tafiyar da harkokin kuɗi na gwamnati ba, musamman idan aka yi la’akari da raguwar kuɗaɗen shiga da ƙasar ke samu cikin sauri da kuma tasirinsa kan kasafin kuɗin shekara.
Babban mai binciken kuɗi, a rahotonsa na shekara-shekara na baya-bayan nan kan yadda ake tafiyar da harkokin kudi na hukumomin gwamnati, wanda a halin yanzu yake gaban majalisun tarayya guda biyu, ya bayyana cewa hukumomi sun kashe kuɗaɗe da yawansu ya kai Naira biliyan 105.66, ta hanyar saɓa ƙa’idoji.
Rahoton ya bayyana cewa, an bayar da Naira biliyan 18.36 na kwangila ba tare da la’akari da dokar gwamnati ba.
