Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu mazauna jihohin Kogi, Neja da Nasarawa sun shawarci gwamnatocin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu su sanya hannun jari a kafa ƙananan na’urorin samar da wutar lantarki masu zaman kansu domin bunƙasa samar wutar lantarki a Nijeriya.
Wannan a cewarsu, zai taimaka wajen magance katsewar tsarin samar da wutar lantarki na aasa da kuma mummunan tasirinsa ga tattalin arzikin ƙasar.
Masu ruwa da tsakin sun yi wannan kiran ne a wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya gudanar a ranar Talata.
Wani kwararre kan harkokin lantarki a Lokoja, Kogi, Joseph Adedayo, ya ce kafa ƙananan na’urorin samar da wutar lantarki masu zaman kansu zai yi matuƙar rage taɓarɓarewar wutar lantarki a ƙasar nan.
Ya ƙara da cewa, idan har jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, za su gina ƙananan gidajen wutar lantarkin nasu, za a magance matsalar wutar lantarki.
Adebayo ya ɗora laifin ƙalubalen wutar lantarki da ake fama da shi a halin yanzu a kan raunin bin ƙa’idoji da kuma rashin ingantattun tsare-tsare, wanda a cewarsa ya kawo cikas ga ci gaban cibiyoyin samar da wutar lantarki mallakar gwamnati.
Masanin ya kuma yi nuni da cewa rashin isassun ƙarfin samar da wutar lantarki na kawo koma baya ga ci gaba da haɓaka a fannin, wanda hakan ya sa jihohi ke da shan wuya wajen kafa cibiyoyin samar da wutar lantarki masu zaman kansu.
Ya kuma ƙara da cewa, matsalar kuɗi ta kuma kasance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana Jihohin ƙasar shiga harkar samar da wutar lantarki.
A cewarsa, kafa tashar samar da wutar lantarki da kuma kula da ita na buƙatar zuba jari mai tsoka, wanda zai iya zama ƙalubale ga jihohin da ke da ƙarancin kuɗi musamman Jihohin da suka dogara kacokan kan kason da gwamnatin tarayya ke samar musu.
“Rashin tsaro da yawaitar lalata kayayyakin wutar lantarki na haifar da babban haɗari ga saka hannun jari a kamfanonin samar da wutar lantarki masu zaman kansu.
“Wadannan ƙalubalen sun nuna irin sarƙaƙƙiyar da ke tattare da harkar wutar lantarki a Nijeriya da kuma buƙatar yin gyare-gyare gadan-gadan don bai wa jihohi damar haɓaka tashoshin wutar lantarkin nasu yadda ya kamata,” inji shi.
Ya buƙaci gwamnati a dukkan matakai da su tabbatar da tsaron kayayyakin wutar lantarki domin daƙile barna da zagon ƙasa.
ƙwararren ya kuma shawarci jihohin da su ƙara himma wajen saka hannun jari a ƙananan hukumomi.
