Tinubu na neman yi wa Dokar Zuba Jari ta 2023 kwaskwarima

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rubutawa Majalisar Dokoki ta ƙasa, inda ya nemi a yi wa dokar kafa Hukumar Kula da Zuba Jari ta ƙasa ta 2023 garambawul.

Buƙatun Tinubu na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka aika wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Talata.

Wasiƙar tana ƙunshe da ƙudirin gyara mai suna: “Gyara Dokar Kada Hukumar Kula da Zuba Karo Ta ƙasa ta 2023, domin la’akari da majalisar dokoki ta ƙasa.”

“A bisa ga sashe na 58 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, na gabatar da haka, saboda kyakkyawan nazari da amincewa da majalisar dattawa ta yi, za a iya yi wa dokar hukumar kula da zuba jari ta 2023 garambawul.”

Tinubu ya ce, manufar ƙudirin dokar ita ce sanya rajistar zamantakewar al’umma ta ƙasa ta zama ginshiƙi na farko don aiwatar da shirye-shiryen saka hannun jari na gwamnati.

Wannan, ya ce zai tabbatar da shirye-shiryen jin daɗin jama’a da kuma aiwatar da bayanai cikin sauƙi.

A cewarsa, gyaran zai tabbatar da tafiyar hukumar tare da samar da fa’ida mai inganci ga ‘yan Nijeriya masu rauni.

By ukarofi