Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ
Mene ne rai ko ruhi? Wannan tambaya ce da ta shige ma ɗan adam duhu tun farkon halittarsa. Ɗaiɗaikun mutane da addinai da dama sun yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun gano bakin zaren wajen fahimtar rai. Amma babu wani addini da ya iya kawo cikakken bayani kafin zuwan Musulunci.
Kafiran Makka, Yahudawa da Nasara na ƙalubalantar Annabi (SAW) da ya kawo musu mu’ujiza kamar yadda Allah ya ba mu labari cikin Suratul Ankabut Q29:50 “Kuma su ka ce “Don me ba a saukar masa da ayoyi (na mu’ujiza) daga ubangijinsa”, sai Allah ya ba su amsa a cikin aya ta gaba inda ya ce Q29:51 “Shin bai ishe su ba cewa lallai mu, mun saukar da littafi a kanka, ana karanta shi a kansu.”
Allah na tabbatar mana da cewa, Annabi bai zo da wata mu’ujiza face Ƙur’ani ba, domin dai shi ummiyi ne, wato bai iya karatu ba ballantana rubutu, amma ya zo da littafin da ke ƙunshe da ilimi na kowanne fanni wanda ba a taɓa jin irinsa ba, kuma ba za a taɓa ji ba. An saukar da wannan littafi a guggutsure tsawon shekaru 23, amma babu wata aya guda da aka saukar a shekarar farko a Makka, wacce za ta ci karo da wata ayar da aka saukar bayan shekaru 20 a Madina. Kuma kama daga fannin zamantakewa zuwa nahawu, kimiyya, tarihin mutum da asalin halitta babu inda aka bari a baya. Allah ya ce, Q6:38 “Ba mu yi sakacin barin komai ba cikin littafi”.
A cikin ƙarni na bakwai sanda aka saukar da littafin, duniya na cikin duhun jahilci, domin dai addinan yYahudu da Nasara sun gurɓace, an yi watsi da ainihin koyarwar littatafan. Amma kasancewar duk da haka babu wanda ya fi Yahudu da Nasara ilimi a wannan zamani sai suka fara ƙalubalantar Annabi da tambayoyi na ilimi.
Akwai jerin tambayoyi, musamman guda uku da suka ce idan dai shi annabi ne, lallai zai iya ba su amsa, saboda sun daɗe su na son amsoshin waɗannan tambayoyi kuma an ce musu sabon annabin da zai zo shine kaɗai zai iya ba su cikakkiyar amsa. Lokacin da su ka zo su ka mika waɗannan tambayoyi guda uku ga Annabi (SAW) sai ya ce musu su dawo gobe zai ba su amsa.
Kasancewar Allah na son mu fahimci mahimmancinsa a rayuwarmu kuma ya nuna ma na cewa, annabawa ma na iya yin kuskure, ko da yake kuskurensu ba na zunubi ba ne kuma ba sa gushewa sai Allah ya kautar da su daga wannan kure. Dalilin haka sai ya ƙi sanar da Annabi amsoshin tambayoyin har tsawon makonni ta yadda kafirai suka riƙa zunɗen Annabi su na cewa, ai maƙaryaci ne. Dalilin wannan ne Allah ya ja masa kunne a cikin Suratul Kahaf Ƙ18:23; “Kada ka ce a game da komai “lallai ne gobe zan yi”.
Ɗaya daga cikin tambayoyin da su ka yi ita ce, mene ne rai ko ruhi? Cikin Suratul Isra sai Allah ya ba da amsar Q17:85 “Su na tambayar ka game da ruhi, ka ce, “Ruhi daga al’amarin ubangijina ne. kuma ba a ba ku (komai) ba daga ilimi face kaɗan”.
Tun da Allah ya halicci duniya zuwa yanzu babu wani mahaluki da zai ce ya fahimci yadda rai ya ke, domin dai iliminsa kaɗan ne Allah ya sanar da mu. Shi rai wani keɓaɓɓen muhalli ne na Allah domin shine sirrin rayuwa kuma shi ne ke tabbatar da cewa babu wani mahalicci sai Allah.
Na farko dai daga wajen Allah rai ya samo asali, kamar yadda ya ba mu labari cikin Suratul Hijiri yayin da Allah ya shirya halitta a doron ƙasa kuma ya ke bai wa mala’iku labari cewa, Ƙ15:29 “To idan na daidaita shi (wato Adam) kuma na hura ruhina a cikinsa to ku faɗi gare shi kuna masu sujjada.”
Ruhi ya samo asalinsa daga Ubangiji, domin ruhin Ubangiji da ya hura ga Adam shine asalin rayuwa a wannan duniya tamu, haka kuma kowanne mahaluki ba ya samuwa sai daga wannan ruhi na Ubangiji kamar yadda ya ce mana cikin suratul Sajda Q32:8-9 “Sannan ya sanya yayansa daga wani asali na wani ruwa walakantacce. Sannan ya daidaita shi kuma ya hura a cikinsa daga ruhinsa, kuma ya sanya muku ji da gani da zukata. Godiyarku kaɗan ce ƙwarai.”
Don haka kowannenmu ba zai iya samuwa ba sai daga wannan ruhi da Allah ke busawa daga gare shi, wannan shi ya sa ruhi ya fi ƙarfin duk waɗansu hanyoyi na sadarwa da Allah ya hore ma na, domin ba mu iya jin sa, ɗanɗanar sa, ganin sa ballantana ma mu taɓa shi. Kawai dai mu na iya sanin ya na nan ko kuma ba ya nan ta hanyoyin gane abu rayayye da matacce.
Duk inda mai rai ya ke sai mu san akwai rai kuma duk inda matacce ya ke mun san cewa rai ya fita. Ilimin ruhi ƙalilan ne Allah ya sanar da mu. Allah ya ƙalubalanci dukkan halittu da cewa, wanda duk ya ce akwai Allah bayan Allah to hanya guda ɗaya tilo da za a bambance allolin ƙarya da Allah na gaske shine kamar yadda ya ce mana cikin Suratul Hajj Q22:73 “Ya ku mutane ga wani misali, sai ku saurara zuwa gare shi, lallai waɗanda ku ke kira baicin Allah, ba za su iya halitta ƙuda ba, ko da sun tattaru (da taimakon juna) domin hakan.”
Don haka idan da wani wanda zai iya halittar ƙuda to bismillah, kuma idan har ya iya yi, to za mu sallama ma sa, amma babu wanda zai iya, domin Allah ya ɓoye wannan ilimi domin ya tabbatar wa masu imani cewa shi kaɗai ne “IIahi”.
Masana kimiyya tsawon shekaru sun yi iya ƙoƙarinsu wajen samar da halitta mai rai daga abubuwa marasa rai, amma sun kasa kamar yadda su ka tabbatar cikin kundin nazarin kimiyyar halittar rayuwa (Encyclopaedia of Biological Science) cewa, “Dukkan wani ƙoƙari na samar da halitta mai rai kai ko ma wani sashe na halitta mai rai daga abubuwa marasa rai ta hanyar binciken kimiyya ya ci tura.”
Cikin fitattun masana kimiyya da su ka ɓata shekaru wajen binciken samar da halitta mai rai, akwai Stanley Miller, wanda bayan gazawa ga abinda ya ce, “Haƙiƙa gano yadda rai ya samo asali ya kasance wata matsala da ta tabbata gagararriya fiye da yadda ni da mutane da dama su ka ɗauka”.
Haka nan Simon Conway shi ma cewa ya yi, “haƙiƙa an kasa samar da rai a ɗakin bincike, kuma babu wata alama da cewa za a iya yi nan gaba… Samuwar rai wani al’amari ne gagara misali, sai dai kawai mu ce samuwar rai mu’ujiza ce.”
Abokin binciken Stanley Miller, wato Francis Crick, wanda su ka yi shekaru gommai na wannan bincike, shi ma cewa ya yi, “duk wani mai faɗar gaskiya, da ya ke da ilahirin ilimin da mu ke da shi a yanzu, zai sallama cewa haƙiƙa yadda rai ya samu a doron ƙasa abu ne da kawai sai dai a kira shi da mu’ujiza.”
Don haka duk yadda mu ka kai ga ilimi ba za mu iya gane sirrin rai ko ruhi ba face ɗan ƙalilan da Allah ya sanar da mu. Rai abokin tagwaitar mutuwa ne, saboda duk lokacin da babu guda akwai gudan. Shi kuma ruhi tun sanda Allah ya fara halittar sa ya na nan a raye sai dai kawai ya na bayyana ne a matsayin rai a lokacin da aka haɗa shi da jiki, amma da zarar an cire shi daga jiki sai ruhin ya kasance a matsayin mutuwa.
Shi ya sa Allah ya ce mana cikin Suratul Baƙara Q2:28 “Ya ya ku ke kafirta da Allah, alhali kun kasance matattu sai ya rayar da ku, sannan ya sanya ku ku mutu sai ya sake rayar da ku, kuma gare shi za ku koma.”
Wato dukkanmu za mu fuskanci mutuwa biyu da rayuwa biyu. Domin bayan Allah ya halicci dukkan rayuka kuma ya shaidar da su kan mulkinsa sun kasance a yanayi na mutuwa kafin a haɗa kowanne ruhi da gangar jikinsa (mutuwar farko). Da zarar jiki ya sami ruhi sai ya zama rayayye (rayuwar farko), sannu a hankali kuma sai kowanne mai rai ya ɗanɗani mutuwa (mutuwa ta biyu), sannan a lahira kuma ranar tashin ƙiyama sai a busa wa kowa rai (rayuwa ta biyu kenan).
Saboda irin ƙauna da Allah ke wa bayinsa bai bar mu cikin duhu ba, don haka don ya na son mu fahimci rayuwa da mutuwa sai ya tsara mu kamar haka Q39:42 “Allah ne ke karɓar rayuka a lokacin mutuwarsu, waɗanda ba su mutu ba kuma (ya karɓa ) a cikin barcinsu. Sannan ya riƙe wanda ya hukunta mutuwa a kansu, kuma ya saki ragowar zuwa ga ajali ambatacce. Lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani.”
Kamar yadda Bahaushe ne ke cewa, “barci ƙanin mutuwa”. Wato a lokacin kowanne barci a na yin ’yar ƙaramar mutuwa ne, don Allah na karɓar rai ne sai barci ya kwashe ka. Wanda duk lokacin barcinsa ya dace da na ajalinsa shi ke nan babu tashi sai dai ya yi tazarce, amma wanda ke da sauran kwana sai a mayar masa da ran sa ya farka.
Shi barci babu wanda zai ce ya san takamaimai lokacin da zai ɗauke mutum sai dai kawai ya sace ka, kamar yadda mutuwa ita ma ba ta sallama sai dai ta zo bakatatan. Haka nan ita ma farkawa ba ka sanin zuwanta sai dai wani abu ya farkar da kai kwatsam. Saboda haka barci da farkawa abubuwa ne guda biyu da Allah ya halitta a jikinmu, don su tabbatar ma na da cewa lallai akwai mutuwa da tashin ƙiyama, wato barci tamkar mutuwa, haka nan farkawa tamkar tashin ƙiyama.
Allah ya ba mu labarin cewa, Q36:52 “Su ka ce “Ya bonenmu! Wane ne ya tayar da mu daga barcinmu?” Wannan shi ne abinda mai rahama ya yi wa’adi da shi kuma mazanni sun yi gaskiya.”
Wato mutuwa tamkar barci ta ke kamar yadda wannan aya ke ba mu labarin cewa, a ranar lahira kafirai idan an tashe su a rayuwa ta biyu bayan wannan, sai su yi ƙorafin wa ya tashe su daga barcinsu, wato mutuwarsu.
Wani gagarumin abu da Allah ya ta’allaƙa da barci kuma shine mafarki; shi mafarki ba a banza aka hore ma na shi ba sai don Allah ya daɗa tabbatar ma na da cewa, duk abubuwa da annabawa su ka zo da shi don kira da gargaɗi da sakamakonsu gaskiya ne (wato yadda rayuwar lahira za ta kasance).
A cikin mafarke-mafarkenmu, duk da cewa mu na kwance a wani gefe guda sai rayukanmu su riƙa yin abubuwa na ban mamaki da a zahiri ko kusa ba za mu iya yi ba. Haka nan mu na iya jin daɗin gaske a mafarki (cin abinci ko jima’i ko farin ciki) ko kuma mu fuskanci matsananciyar wahala (yunwa, asara ko fargaba) yadda mu na farkawa za mu cigaba da jin abinda ya faru a mafarkin kafin mu gane cewa, ashe mafarki ne. A taƙaice dai Allah na son mu fahimci cewa barci, mafarki da farkawa a kullum rana da Allah ya wajabta a tsarin rayuwarmu, an yi su ne domin su riƙa tuna mana ko jaddada mana rayuwar duniya, mutuwa da rayuwar lahira ne.
Sadiƙ manazarci ne a Kano
