Ranar Mata: Za mu inganta muradun mata – Shugaban INEC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce, za ta cigaba da inganta muradun mata tare da yin haɗin gwiwa da su, domin gudanar da sahihin zaɓe na gaskiya da adalci a siyasance.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan alƙawarin a cikin wata sanarwa ranar Talata a Abuja, don bikin Ranar Mata ta Duniya.

Yakubu ya ce, hukumar ta daɗe tana neman duk jam’iyyun siyasa da suka yi rajista, don inganta damar samun dama ga mata zuwa muƙaman zaɓe.

“INEC ta haɗa kai da miliyoyin matan Nijeriya da sauran takwarorinsu na duniya domin murnar wannan rana ta musamman domin la’akari da babbar sadaukarwar da suka yi wajen gina ƙasa, samar da dimokuraɗiyya da kuma kiyaye martabar iyali a ƙasar.

Taken wannan shekara shi ne ‘Daidaita jinsi a yau don ɗorewar gobe’, wanda ya yi daidai da amincewar hukumar kan muhimmancin haɗa kai.

“Haka kuma ya yi daidai da buƙatar ƙarfafa gwiwar mata da su shiga harkar zaɓe. Saboda haka ne hukumar ta samar da wani sashe na musamman na kula da jinsi da haɗa kai domin kula da muradun mata.

“Hukumar ta kuma yi ta duba duk jam’iyyun siyasa masu rijista a Nijeriya don inganta damar da mata za su samu zuwa muƙamai masu zaɓe.

“Hukumar za ta ci gaba da inganta muradun su tare da yin haɗin gwiwa da su domin gudanar da zaɓe cikin ’yanci, gaskiya da adalci,” inji Farfesa Yakubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *