Ranar musamman ga Sin da Nijeriya

Daga LUBABATU LEI

Yau ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 73 da kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin, wadda kuma ta yi daidai da ranar cika shekaru 62 da samun ‘yancin kan Nijeriya, ranar da ta alakanta ƙasashen biyu da ma al’ummunsu ta wata hanya ta musamman, duk da nisan da ke tsakaninsu.

Tun bayan da ƙasashen biyu suka kulla hulɗar diplomasiyya a shekarar 1971, sun aiwatar da haɗin gwiwa ta fannonin siyasa, da tattalin arziki, da al’adu, da kimiyya da dai sauransu, tare da cimma gaggaruman nasarori.

A ranar 1 ga watan Yulin bana, jirgin ruwa na farko ya isa tashar ruwa ta Lekki da ke Lagos wadda ake ginawa, daga bisani, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa, inda ya bayyana murna, da farin ciki, game da yadda jirgin ya isa wannan tashar ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, wadda kamfanin ƙasar Sin ke ɗaukar nauyin ginawa.

Ya ce, tashar za ta samar da ɗimbin guraben aikin yi bayan da aka fara aiki da ita, baya ga kuma yadda za ta kyautata rayuwar al’ummar Nijeriya, tare da sa ƙaimi harkokin cinikayya a tsakanin Nijeriya da ƙasashen ƙetare, wanda hakan zai taimaka ga kyautata yanayin kasuwanci na ƙasar tare da janyo ƙarin jarin waje.

A watan Agustan da ya gabata kuma, ƙasashen biyu sun cimma yarjejeniyar kafa tsarin haɗin gwiwa a tsakanin asibitin jami’ar Peking ta ƙasar Sin, da ma asibitin jami’ar Abuja na Nijeriya, a wani ƙoƙari na inganta haɗin gwiwar ƙasashen biyu ta fannin kiwon lafiya.

Sai kuma a watan Agusta, lokacin da aka ƙaddamar da mataki na biyu na aikin kafa fitilu masu amfani da hasken rana na ba da hannu ga motoci a birnin Abuja.

Dukkan waɗannan wani ɓangare ne kawai na nasarorin da aka cimma a haɗin gwiwar ƙasashen Sin da Nijeriya.

Da tashar ruwa ta Lekki, da layin dogon Abuja-kaduna, da filin jiragen sama na Lagos, da tashar samar da wutar lantarki ta Zungeru, da kuma musayar kuɗaɗe tsakanin ƙasashen biyu, da haɗin gwiwar harba taurarin dan Adam da binciken teku, lallai haɗin gwiwar ƙasashen biyu ya shafi fannonin tattalin arziki, da al’adu, da ba da ilmi, da kiwon lafiya, da hada-hadar kuɗi, da kimiyya da sauransu, wanda ya haifar da haƙiƙanin alfanu ga al’ummar ƙasashen biyu.

Ranar 1 ga watan Oktoba, ta shaida yadda ƙasashen biyu suka yi gwagwarmayyar fita daga mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki a baya, tare da bude sabon babinsu.

Muna da imanin cewa, bisa shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, da ma tsarin dandalin haɗin gwiwar Sin da Afirka, ƙasashen biyu za su ƙarfafa dankon zumunci tsakaninsu, kuma haɗin gwiwar ƙasashen biyu zai haifar da ƙarin nasarori, da ma alfanu ga al’ummunsu.

Mai Zane: Mustapha Bulama