Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun gudanar da gangamin siyasa a ƙofar shiga gari da ke Lekki a Jihar Legas.
Wannan na zuwa ne duk da umarnin da kotu bayar kan kada su kuskura su gudanar da gangami a yankin.
An ga magoya bayan Peter Obi sun yi dandazo a ƙofar Lekki a safiyar Asabar, 1 ga Oktoban 2022.