Benzema ya koma atisaye bayan jinyar da ya yi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Real Madrid ta fara atisaye a shirin da ta ke na fuskantar wasan La Liga karawar mako na bakwai da za ta karvi baƙuncin Osasuna ranar Lahadi.

Cikin waɗanda suka yi atiaye a safiyar nan har da ɗan ƙwallon tawagar Faransa, Karim Benzema, wanda ya sha jinya.

Ɗan ƙwallon ya ji rauni a wasan da Real Madrid ta je ta doke Cetic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar 6 ga watan Satumba.

Benzema, wanda ya buga wa Real Madrid wasa biyar har da Champions League ɗaya a bana ya ci ƙwallo uku.

Ɗan wasan ya yi atisaye ƙarƙashin Ancelotti ranar Laraba, wanda ya samu halartar wasu ‘yan ƙwallon, bayan da suka buga wa tawagoginsu wasanni.

Waɗanda suka koma atisaye har da Courtois da Hazard da Camavinga da Alaba da Mendy da Tchouameni da kuma Rudiger.

Lucas Vazquez na ci gaba da murmurewa, yayin da Modric ya motsa jiki a rufaffen ɗaki.