Majalisar gudanarwar Sin ta gudanar da liyafa domin murnar ranar kafuwar ƙasar

Daga CMG HAUSA

Majalisar gudanarwar ƙasar Sin ta gudanar da liyafa a babban ɗakin taron jama’a dake birnin Beijing a jiya, domin murnar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin dake gudana a ranar 1 ga watan Oktoba.

Da yake jawabi ga taron liyafar, firaministan Sin Li Keqiang, ya ce JKS za ta gudanar da babban taron wakilanta karo na 20 a bana, yana mai jaddada muhimmancin taron.

A cewarsa, tabbatar da kyakkyawan tubalin tattalin arziki na da matuƙar muhimanci ga ɗorewar ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

Ya kara da cewa, ƙasar Sin za ta ɗauki managartan matakai na sauƙaƙa raɗaɗin ƙalubalen da ba a yi tsammani ba tare da aiwatar da manufofin da suka dace a kan lokaci, domin daidaita tattalin arzikin.

Yana mai cewa, suna da ƙwarin gwiwa da ƙarfin tabbatar da daidaituwar manyan alkaluman tattalin arzikin bisa matakin da ya dace.

Ya ce bisa manufar buɗe ƙofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, ƙasar ta samu nasarori a fannin yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki irin na gurguzu, da ƙara buɗe ƙofa da karfafa cinikayya da zuba jari da ƙasashen waje da zurfafa haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ƙasa da ƙasa, domin ƙasar Sin ta ci gaba da kasancewa wuri mafi dacewa na zuba jari da samun ci gaba irin na moriyar juna.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha