Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (2)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, idan mai karatu bai manta ba, mun fara da kawo rashe-rashen da aka yi a masana’antar fim ta Arewacin Nijeriya, wato Kannywood. A wannan satin, za mu ci gaba ne ta hanyar kawo na ɓangaren takwarorinsu da ke Kudu, wato Nollywood:

Idan muka juya ɓangaren masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood, shekarar 2022 ta tafi bayan ta bar masu tabo na daga mutuwar matasa da kuma tsofafi daga cikin wannan masana’anta. Daga watan Junairu zuwa Disamba, an ruwaito mutuwar iyalan wannan masana’anta har 17, waɗanda kansu za mu yi waiwaye da kuma irin rawar da suka taka a masana’antar;

Lari Williams:

Lari Williams

Sanannen jarumi a masana’antar Nollywood, Lari Williams ya kasance jajirtaccen ɗan wasa da ya kafa tarihi a masana’antar, kasancewarsa jarumi na farko da ya hau saman dutsen Zuma Rock na Birnin Tarayya mai tsayin ƙafa 1,200, ba don komai ba sai don ɗaukar shirin fim. Haka kuma shi ne shugaba na farko a Ƙungiyar Actors Guild Nigeria.

Yana ɗaya daga cikin jaruman da suka taka rawa a tsohon shirin fim ɗin nan na ‘Village Headmaster’. Kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka haska fim ɗin gida na farko da aka taɓa yi a Nijeriya, mai suna, ‘The Witch Doctor’.

A ɓangare ɗaya ya kasance mai ilimi a harkar fim, inda ya koyar da ilimin a jami’ou uku da ke cikin Nijeriya, Jami’ar Iko, wato University of Lagos, sai Lagos State University da kuma University of Calabar.

Lari Williams ya mutu a ranar 28 ga watan Fabraru, 2022, wanda ya yi daidai da cikar sa shakara 81 a duniya.

Tafa Oloyede:

Tafa Oloyede

Jarumi John Adewuni Adewoye, wanda aka fi sani da Tafa Oloyede, an haife shi a ranar 19 ga watan Nuwamba, 1952, ya tsunduma a harkar fim a shekarar 1974, a ƙarƙashin marigayi Oyin Adejobi.
Ya fito a finafinai da dama waɗanda suka haɗa da; ‘Ayanmo’, ‘Ekuro Oloja’, ‘Orogun’, ‘Akanji Oniposi’ da dai sauran su.

Tafa Oloyede ya mutu a ranar 2 ga watan Fabrairu, shekarar ta 2022, kuma ya mutu ne yana da shekaru 69 da haihuwa.

Romanus Amuta:

An sanar da mutuwar jarumi Romanus Amuta a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2022, bayan ya yi fama da rashin lafiya ta tsawon lokaci. Ya mutu yana da shekara 79. Ɗaya daga cikin finafinansa da suka yi fice shi ne, ‘New Masquerade’, wanda aka ɗauka tun a ƙarni na 80.

Takor Veronica:

Takor

Ɗaya daga cikin mutuwar da ta jijjiga masana’antar Nollywood akwai mutuwar jaruma Takor Veronica, wadda aka riski gawarta a ɗakin wani otel da ke Benue, kwanaki ƙalilan bayan ta gama bikin zagayowar ranar haihuwarta.

Marigayiyar ta yi shagalin bikin haihuwar tata a ranar 12 ga watan Maris, 2022, kwanaki ƙalilan da mutuwarta. Duk da cewa, ba a san musababin mutuwar jarumar ba, sai dai abokanai da kuma masoyan jarumar sun matuƙar nuna alhininsu, yayin da suka karaɗe kafafen sada zumunta da hotunanta da kuma kalamai masu sosa zuciya.

Shade Akintalor:

Magbojo

Shahararriyar yar wasan Yarbanci da sunanta ya yi fice Shade Akintaylor, wadda aka fi sani da Oluweri Magbojo, ta mutu ne a ranar 1 ga watan Maris, 2022. Jarumar ta mutu ne tana da shekara 59, a Ƙasar Burtaniya.

Iyalanta ne suka bayyana labarin mutuwarta, sai dai ba su bayar da wani bayani kan ko ta yi ciwo ne da kuma abinda ya zama silar mutuwarta. Ɗaya daga cikin finafinan da za a iya tunawa da marigayiyar akwai ‘Oluweri Mabo Ojo’, wanda anan ne ta samu laƙabin da ake yi mata na Oluweri Magbojo.

Dejo Tunfulu:

Masana’antar Nollywood ta shiga jimami a ranar 1 ga watan Afrilu, 2022, sa’ilin da labarin mutuwar fitaccen jarumin Yarbanci, Dejo Tunfulu, ta riske su.

Marigayin ya kasance jarumin barkwanci da ake haskawa a finafinan yaren Yarbanci. Baya ga haka shi marubuci ne kuma mai shirya fim a masana’antar.

Dejo Tunfulu, wanda ake wa inkiya da Kunle Mac-Adetokunbo, ya fara harkan fim tun a farkon samarta, inda ya fara da wasan kwaikwayo na gidan talabijin, kafin a fara ganin shi fim ɗinsa na farko mai suna ‘Aje ni Iya mi’. Jarumin ya mutu yana da shekaru 49.

Chinedu Bernard:

Bernard

Jarumar da ta yi suna da kyau da iya wasan kwaikwayo, Chinedu Bernard, mutuwarta ta zo da al’ajabi, inda rahotanni suka ruwaito cewa, ta sulale ta faɗi a mace, yayin da ta ke goge-goge a Cocin St. Leo the Great Catholic Church da ke Jihar Inugu, a ranar 29 ga watan Afrilu, 2022, bayan an yi gaggawar isa da ita asibiti mafi kusa da Cocin inda suka tabbatar da mutuwar tata.

Jarumar wadda asalinta ‘yar Jihar Inugu ce, an haife ta a ranar 29 ga watan Mayu, kuma ta mutu a shekarunta na ƙurciya. Za a iya tunawa da Jaruma Chinedu da finafinai kamar haka; ‘The Regret’, ‘Royal Bracelet’, ‘Onlocked’, ‘My Sister’s Man’, ‘Love Without Conscience’, ‘Just A Wish’, ‘Money Fever’, ‘Who Runs The City’ da dai sauran su.

David Osagie:

David Osagie

Mutuwar Jarumi David Osagie ta zama jerin mutuwar bazata da ta samu Nollywood a shekarar 2022, domin ya mutu awanni bayan bayyanar sa a wurin shirya fim, kuma ya yi shirin na ranar, bayan kammala aikin a ranar, ya je gida, ya kwanta, daga nan ba a ta shi da shi ba. An tabbar awannin da ke tsakanin dawowar shi da mutuwar ba su kai awa 24 ba.

An samu labarin mutuwar Jarumi David Osagie ranar Laraba ta hannun abokin aikinsa Ngozi Ezeh.


“Cike da jimami na ke sanar da rashin sarki a Nollywood da muka yi, Sir David. Mutuwa ce ba tare da rashin lafiya ba, ya dai kwanta, ba a tashi da shi ba, ” inji Ngozi Ezeh.

Jarumi David Osagie ya mutu a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu, 2022, duk da cewa, a daren Talata ne da ya kwanta barci ake hasashen mutuwar tasa.