Rashin aiki a Nijeriya ya kai kashi 33.3, cewar NBS

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya (NBS), ta ce aƙaluman rashin aiki a Nijeriya sun sake cillawa, kamar yadda wani rahotanta ya nuna bada jimawa ba.

Rahoton hukumar ya nuna an samu ƙarin adadi na rashin aiki a Nijeriya da ya kai kashi 33.3 cikin ɗari a zango na huɗu a 2020 saɓanin kashi 27.1 cikin ɗari a zango na biyu a 2020.

NBS ta sanar da haka ne a cikin rahotonta da ta shirya kan sha’anin ƙwadago, tare da la’akari da matsalar rashin aiki musamman kuma a zamanin da ake fama da cutar korona, inda ta gano tsanantar da rashin aiki ya yi a ƙasa.