Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Karuwar tasirin hamshaƙin attajirin nan, Aliko Dangote, a ɓangaren kasuwar man fetur ta ƙasa na ci gaba da haifar da cece-kuce, rikicin shari’a da damuwa tsakanin hukumomi, :yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki kan fargabar yiwuwar komawar harkar man fetur ta Nijeriya ƙarƙashin ikon kamfani guda.
A tsakiyar muhawarar akwai sabon ƙarar da Matatar Dangote ta shigar a kotu kan Babban Lauyan Tarayya, tana ƙalubalantar lasisin shigo da man fetur da aka bai wa ’yan kasuwa da Kamfanin Man Fetur na ƙasa, wato NNPC.
Rikicin ya sake tayar da tattaunawa a faɗin ƙasa kan ko harkar man fetur ta Nijeriya na komawa wani yanayi da matata guda za ta mamaye samar da mai, tasiri kan farashi da kuma iko da kasuwa, lamarin da zai iya raunana ƙananan ’yan kasuwa da rage gasa a kasuwar mai.
Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Mam Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta bai wa kamfanoni shida lasisin shigo da fetur, tana mai cewa har yanzu ana buƙatar man da ake shigo da shi daga ƙasashen waje domin cike giɓin samar da mai da kuma hana ƙarancin mai a ƙasa.
Sai dai Matatar Dangote ba ta amince da wannan matsaya ba. A cikin takardun ƙarar da aka gani, matatar na neman a soke lasisin shigo da man da aka bai wa NNPC da wasu kamfanonin kasuwancin mai, tana mai cewa hakan ya saɓa wa tanade-tanaden doka tare da raunana ƙoƙarin tace mai a cikin gida.
Wannan ƙarar ba ita ce ta farko ba. A shekarar 2025, Matatar Dangote ta janye irin wannan ƙara bayan sa bakin gwamnatin tarayya. Sai dai sabon matakin shari’ar na nuna cewa rikicin tsakanin matatar, hukumomi da masu kasuwancin mai bai ƙare ba.
Babbar tambayar da ake yi yanzu ita ce: ya kamata Nijeriya ta ci gaba da barin shigo da mai daga ƙasashen waje alhali Matatar Dangote na iƙirarin cewa tana da aarfin biyan buƙatar cikin gida?
Ga Dangote, amsar a bayyane take. Attajirin ya sha bayyana cewa babu dalilin ci gaba da shigo da fetur yayin da tankokin matatarsa ke cike da mai. Amma ga hukumomi da ‘yan kasuwa, lamarin ya fi haka rikitarwa. Ko da yake ana kallon Matatar Dangote a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin masana’antu a Afirka, ana nuna damuwa cewa dogaro da kamfani guda wajen samar da mai na iya jefa kasuwar Nijeriya cikin haɗari a nan gaba.
Masana harkar makamashi sun bayyana cewa ko da matatar na da girma da inganci, bai kamata kamfani guda ya mamaye kasuwa ba saboda hakan zai iya rage gasa, raunana ƙananan masu kasuwanci da haifar da matsala wajen rarrabawa da farashi.
Wasu daga cikin kamfanonin da NMDPRA ta bai wa lasisin shigo da mai sun haɗƙ da NIPCO, AA Rano, Matrix, Shafa, Pinnacle da Bono.
Sai dai masu kasuwancin mai sun nuna damuwa cewa idan aka hana shigo da mai gaba ɗaya, ƙananan kamfanoni za su zama masu dogaro kacokan da Matatar Dangote wajen samun mai da farashinsa.
Kamfanin NNPC ma ya nuna adawa da ƙarar Matatar Dangote a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.
A cikin bayanan da ya gabatar, NNPC ya yi gargaɗin cewa hana shigo da mai na iya jefa ƙasa cikin matsalar ƙarancin mai, tashin farashi da kuma barazana ga tsaron makamashi na ƙasa.
Kamfanin ya ce Dokar Masana’antar Mai ta bai wa hukumomi damar bai wa ƙwararrun kamfanoni lasisin shigo da mai, musamman idan akwai buƙatar cike giɓin samar da mai.
NNPC ta kuma ƙalubalanci Matatar Dangote da ta gabatar da sahihan hujjoji masu zaman kansu da za su tabbatar cewa tana iya samar da dukkan buƙatar man fetur ta Nijeriya ba tare da tangarɗa ba.
Farfesa Kennedy Odinwa, masani kan harkar makamashi, ya yi gargaɗi kan yiwuwar mamayar kasuwar mai daga kamfani guda.
Ya ce, duk da irin gagarumar nasarar da Matatar Dangote ta samu, bai dace a bar kamfani guda ya yi ƙarfin da zai raunana gasa da sauran masu zuba jari ba.
“Dangote ba zai iya biyan dukkan buƙatar man Nijeriya shi kaɗai har abada ba. Tsaron makamashi na buƙatar hanyoyin samar da mai masu yawa da kuma gasa mai kyau,” inji shi.
Sai dai duk da cece-kucen, Dangote ya nuna babu alamun janyewa daga manufarsa. A wata hira da ya yi da Nicolai Tangen, attajirin ya bayyana cewa matatarsa ta riga ta fara tace ɗanyen mai fiye da ƙarfinta da aka tsara tun farko. Ya ce, matatar ta riga ta tace ganga 661,000 na ɗanyen mai a rana, yana mai cewa hakan ya tabbatar da ƙarfinta.
Dangote ya kuma bayyana cewa matatar na sayen ɗanyen mai daga Nijeriya, Angola, Libya da Amurka, tare da shirin ninka ƙarfin matatar cikin watanni 30 masu zuwa. Ya kuma zargi wasu masu anfani da tsohon tsarin tallafin mai da shigo da fetur da ƙoƙarin hana matatar nasara.
Dangote ya kira waɗannan mutane da suna “Mafia”, yana mai cewa suna anfani da biliyoyin daloli daga tsarin tallafin mai da kasuwancin shigo da fetur. Ya ce, burinsa shi ne samar da abubuwan da Nijeriya ke shigowa da su daga ƙasashen waje a cikin gida.
Rikicin na yanzu ya nuna babbar gwagwarmaya kan makomar tsarin kasuwar man fetur ta Nijeriya. Shekaru da dama ‘yan Nijeriya na ƙorafi kan dogaro da shigo da mai daga waje, badaƙalar tallafi da rashin wadatattun matatun mai.
Yanzu da aka samu babbar matatar mai ta masu zaman kansu, wata sabuwar damuwa na tasowa — ko maye gurbin dogaro da shigo da mai da mamayar kasuwa daga kamfani guda ba zai haifar da wani sabon matsala ba.
