Rokokin Long March na Ƙasar Sin sun kafa tarihi na harba kumbuna zuwa sararin samaniya

Daga CMG HAUSA

A safiyar yau ne, ƙasar Sin ta yi amfani da rokar Long March-2D wajen harba rukunin taurorin dan Adam zuwa sararin samaniya, wanda ya nuna nasarar da ƙasar ta cimma wajen amfani da rokar wajen harba kumbuna sau 103 a jere.

Nasarorin da aka cimma a baya wajen amfani da rokar ta Long March a jere shi ne 102, wanda aka fara cimmawa daga shekara 1996 zuwa ta 2011.

Tun daga ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2020, rukunin rokar Long March na ƙasar Sin, ya cimma nasarori 103 a jere a cikin watanni 27 kacal, inda ya yi jigilar sama da kumbuna fiye da 200 zuwa sararin samaniya, ciki har da na’urorin binciken tashar sararin samaniya, da na binciken duniyar wata, da duniyar Mars, da kuma kumbo mai ɗauke da ‘yan sama jannati. Kamar yadda hukumar binciken kimiyya da fasahar sararin samaniyar ƙasar ta bayyana.

Hukumar ta ƙara da cewa, ƙasar Sin na ƙera na’urorin harba kumbuna da manyan rokoki, waɗanda za su yi jigilar ma’aikata zuwa duniyar wata a nan gaba, da kara yin balaguro zuwa duniyar Mars, da Jupiter da sauran ƙananan duniyoyi da ake kira asteroids.

Fassarawar Ibrahim