Ana samun sakamako mai kyau a haɗin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka

Daga CMG HAUSA

An gudanar da taron manyan wakilai game da nazarin matakan aiwatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar haɗin gwiwar ƙasar Sin da ƙasashen Afirka (FOCAC) ta yanar gizo a ranar 18 ga wannan wata, inda ɓangarori daban daban suka cimma daidaito kan yadda za a gaggauta gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma a sabon zamani, da inganta haɗin gwiwar abokantaka a tsakanin ƙasashe masu tasowa, da kuma kiyaye amfanin dandalin tattaunawar na FOCAC.

A shekarun baya-baya nan, bisa tsarin dandaloli irin su bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin ƙasar Sin, da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, da bikin sayar da kayayyakin Afirka ta intanet, ƙarin kayayyakin Afirka sun shiga kasuwar ƙasar Sin.

Alkaluman ƙididdiga na nuna cewa, tun bayan taron ƙolin dandalin tattaunawar haɗin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a nan birnin Beijing a shekarar 2018, an ba da izinin shigar da kayayyakin amfanin gona da kayayyakin abinci iri 25 daga ƙasashen Afirka 14 da suka haɗa da ƙasashen Kenya, da Afirka ta Kudu, da Benin, da Masar zuwa ƙasar Sin.

Ƙasar Sin ta kasance ƙasa ta biyu a duniya wajen sayen kayayyakin amfanin gonan ƙasashen Afirka.

A shekarar 2021, yawan kuɗin kayayyakin amfanin gona da ƙasashen Afirka suka sayar wa ƙasar Sin ya ƙaru da kashi 18.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2020.

Ban da wannan kuma, tun bayan da aka kafa dandalin tattaunawar na FOCAC, tsawon hanyoyin jiragen ƙasa da kamfanonin Sin suka gina ko gyara a ƙasashen Afirka ya zarce kilomita dubu 10, tsawon hanyoyin motoci ya kai kimanin kilomita dubu 100.

Yawan gadoji ya kai kusan dubu ɗaya, yayin da yawan tasoshin jiragen ruwa, ya kai kusan ɗari ɗaya, da asibitoci da makarantu da dama, da samar da ayyukan yi fiye da miliyan 4 da dubu 500 a ƙasashen Afirka.

Jama’ar ƙasashen Afirka sun yaba matuka da waɗannan nasarori.

Fassarawar Zainab