Jigo a Jam’iyar APC a Sakkwato, Hajiya ‘Yar Halima ta fice daga jam’iyar zuwa PDP

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Hajiya ‘Yar Halima ta sanar da ficewarta Jam’iyyar APC ne a wani taron da Uwargidan Malam Saidu Umar ta shirya mata a Cibiyar Horas da Matasa ta Youth Center dake Sakkwato.

Hajiya ‘Yar Halima Tudun Wada ta ce ta yanke hukuncin barin Jam’iyar APC saboda rashin alƙibilar siyasa a jam’iyyar da kuma siyasar ubandgida tare da rashin saka mata cikin harkokin siyasa a jam’iyar.

Haka ma ta ce akwai rashin ƙwarewa da ingancin ɗan takara a Jam’iyyar ta APC, inda ta ƙara da cewa gwamnatin APC mataki na ƙasa ta ƙasa magance matsalar tsaro da ya addabi ƙasar nan shi ya sa ta ga ba ta da zavi illa ta canza sheƙa da ita da magoya bayanta.

Hajiya ‘Yar Halima ta bada tabbacin yin aiki tuƙuru domin samun nasarar Malam Ubandoma a zaɓe mai zuwa.

Da take karvar wadda ta canza sheƙar, Uwargidan ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP Hajiya Hindatu Saidu Umar ta bayyana cewa Hajiya ‘Yar Halima ta yi kyakyawar tunani da lokacin da ya dace.

Hajiya Hindatu ta ƙara da cewa idan Malam Ubandoma ya yi nasara a zaɓe mai zuwa zai tabbatar da an ba mata kyakyawar wakilci a gwamnatinsa.

Hajiya Hindatu ta yi alƙawarin yin aiki tare da Hajiya ‘Yar Halima domin samun nasarar Jam’iyyar PDP a kowane mataki.

Sauran matan da suka yi magana a wurin sun haɗa da matar shugaban ƙaramar hukumar Sakkwato ta Kudu, Hajiya Zainab Faruku Sayudi da kuma Shugabar Mata ta PDP na ƙaramar hukumar Hajiya Rabiatu Hassan.