Katsina: Komawar ’yan gudun hijira gidajensu

Babu shakka, Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar rashin tsaro ta fi ƙamari a halin yanzu wanda ya shafi al’ummomi da dama a faɗin ƙananan hukumomin da bai wuce 15 ba.

Mazauna wasu garuruwan Batsari, Safana, Jibiya, Kurfi, Dutsinma, Faskari, Ƙanƙara, Dandume, Funtua da dai sauransu, na ci gaba da fuskantar barazana daga ’yan bindiga da ke kashe mutane, yiwa mata fyaɗe da kuma sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Idan za mu iya tunawa cewa, a wani ɓangare na ƙoƙarin shawo kan wannan annoba, gwamnatin jihar ta yi shawarwari tare da yin afuwa ga wasu ’yan bindiga da suka yi iƙirarin cewa sun tuba kuma suka yi alƙawarin ajiye makamai da kuma daina yin ta’addanci. Amma, hakan ya kasance tuban mazuru ne, domin kuwa yaudara ce don daga baya sun koma dajin sun ci gaba da yin fashi da makami.

’Yan bindigar sun yi ƙaurin suna har suka kai hari a wasu unguwanni a cikin birnin Katsina don yin garkuwa da mazauna garin, lamarin da ya faru na baya-bayan nan shi ne harin da aka kai a unguwar Shola da ke bayan Asibitin Koyarwa na Yar’adua, wanda ke zaman tsohuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.

Ƙalubalen tsaro ya sa mazauna wasu al’ummomin da lamarin ya fi shafa su yi rayuwarsu ta yau da kullum cikin ƙunci. Da yawa daga cikinsu an sanya su zaman kashe wando saboda ba za su iya zuwa gonaki ba.

An tilasta wa wasu yin ƙaura kuma a halin yanzu suna neman mafaka a sansanonin ’yan gudun hijira da aka keɓe.

Babu wani abu da ya nuna girman rashin tsaro kamar yadda ake ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummomi da kuma kasancewar sansanonin ‘yan gudun hijira a sassa daban-daban na jihar ciki har da Jibiya, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da lamarin ya fi ƙamari, inda adadin waɗanda suka rasa matsugunansu, suka nemi mafaka a Jamhuriyar Nijar da kuma jihohin da ke maƙwabtaka da Kaduna da Kano.

Sansanin na Jibiya yana da mutane kusan 6,000 daga Shimfida, al’ummar da ke barci a hanyar Jibiya zuwa Katsina, waɗanda ’yan ta’addan ke ci gaba da kai musu hare-hare. Mun lura cewa hare-haren da ake ci gaba da kaiwa ya tilastawa mazauna garin Shimfida yin ƙaura daga garinsu domin neman tsira.

Akwai rahotannin kafafen yaɗa labarai cewa yayin da aka tsugunar da kusan 6,000 daga cikinsu a Jibiya, wasu kuma sun koma garuruwan da ke maƙwabtaka da Jamhuriyar Nijar.

Watanni biyar bayan gudun hijirar da aka tilasta musu, gwamnatin jihar Katsina ta mayar da kimanin 12,000 daga cikin ’yan gudun hijirar da suka ƙunshi 6,000 kowannen su da suka fake a Jibiya da Jamhuriyar Nijar, zuwa garinsu.

Babu jayayya cewa sansanonin ‘yan gudun hijira shiri ne na wucin gadi da aka sanya don magance buqatun waɗanda abin ya shafa na samun mafaka.

An yi la’akari da cewa abin da ake buƙata shi ne mafita mai ɗorewa wanda ya haɗa da, da sauran matakan da aka ɗauka na mayar da ’yan gudun hijirar zuwa gidajensu na asali. A kan haka ne muke kallon wannan mataki na gwamnatin jihar a matsayin abin yabawa.

Wannan karimcin ya yi daidai da sashe na 28 na ƙa’idojin Jagora game da ƙaura daga cikin gida, da kuma ci gaba da bayar da shawarwarin da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa (NCFRMI) ta yi, game da kasancewar ‘yan gudun hijira na dindindin a sansanonin.

Don jaddadawa, wannan labarin ya bayyana haqqin ‘yan gudun hijirar don samun mafita mai ɗorewa, alhakin hukumomin ƙasa, da kuma rawar da masu aikin jinƙai da ci gaba za su taimaka wajen tabbatar da mafita mai ɗorewa.

Mun yi imanin cewa mafi ɗorewar mafita da ake da ita ita ce a tabbatar da komawar ‘yan gudun hijirar zuwa mazauninsu na asali. Idan aka yi la’akari da wannan al’amari, abin da gwamnatin Jihar Katsina ta yi ya dace kuma abin a yaba ne.

Mazauna Shimfida yawancinsu manoma ne, kuma fiye da komai, ’yan bindiga sun kawo cikas ga ayyukan noma a wannan yanki da sauran al’ummomin da ke can ta hanyar jefa su ga yunwa da fatara.

Idan su ka koma gidajensu, ko shakka babu, za su samu damar ci gaba da harkokinsu na tattalin arziki da kuma rayuwa cikin mutunci.

To sai dai duk da haka muna jinjina wa gwamnatin Jihar kan yadda ta mayar da ’yan gudun hijirar zuwa gidajensu na asali domin su koma rayuwarsu ta yau da kullum, ya dace a yi garaya a kan buƙatar samar da tsare-tsare na tsaro don daƙile ci gaba da kai hare-hare.

Haƙiƙa, wannan kiran ya zama wajibi la’akari da yadda ’yan bindigar, daga rahotannin hare-haren baya-bayan nan, da suka haɗa da na ƙauyen Natsinta da ke kusa da barikin bataliya ta 35, na ci gaba da addabar yankin.

Wannan ya nuna buqatar haɗin gwiwa daga jami’an tsaro daban-daban da suka haɗa da mazan hukumar shige da fice ta Nijeriya tun da Jibiya na kan iyaka kuma yana iya kamuwa da kwararar ’yan ƙasashen waje.

Yanzu da ’yan gudun hijirar suka koma gida, gwamnati, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro dole ne ta tabbatar musu da ingantaccen tsaro, domin ta haka ne kawai za a yi nasara a kan jigon dawowarsu.