Ba ni da niyyar komawa Jam’iyyar PDP – Shekarau

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba shi da niyyar komawa Jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya.

Shekarau ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Sule Ya’u Sule, a tattaunawarsa da BBC Hausa ranar Talata.

A cewarsa, babu ƙamshin gaskiya a rahotannin da wasu kafafen Nijeriya suka bayar cewa ɗan takarar shugabancin ƙasar na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tayin ba shi manyan muƙamai idan ya koma jam’iyyar.

Sule Ya’u Sule ya ce Malam Shekarau, wanda yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ƙasar, yana nan daram a Jam’iyyar NNPP.

Amma ya ƙara da cewa hasashen da ake yi na komawarsa PDP na da nasaba da yadda ɓangaren tsohon gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso ya gaza cika alƙawuran da suka yi a yarjejeniyar da suka ƙulla lokacin da zai shiga NNPP.

Sule Ya’u ya ce idan ban da Sanata Shekarau babu wani daga cikin mutanensa da ɓangaren Kwankwaso ya bai wa wani muƙami ko kujera a yarjejeniyar shigarsa jam’iyyar tasu.

Ya tabbatar da cewa wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga jam’iyyun daban-daban na ƙasar suna tuntubar Sanata Shekarau domin ganin ya koma jam’iyyunsu, ko da yake ba shi da niyyar yin haka.

Ya qara da cewa cikin waɗanda suka tuntuɓe shi har da Atiku Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar LP, Peter Obi; da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.

Shekarau ya ce Peter Obi ya neme shi ne domin ya zama mataimakinsa, yayin da shi kuma Tinubu ya nemi ya koma APC domin ya taka rawa a zaɓen 2023.

A cewarsa, kawo yanzu bai yanke shawara kan ko zai koma wata jam’iyya ba, yana mai cewa sai wani kwamiti mai mutum talatin ya zauna ya yi nazari kafin ya yanke hukunci kan mataki na gaba.