Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan zira ƙwallaye 763 a raga

Daga UMAR M. GOMBE

A halin da ake ciki, Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a tarihin duniyar ƙwallon kafa a matsayin wanda ya fi kowane ɗan wasan yawan zira ƙwallo a raga.

A cewar Marca, Ronaldo wanda dan asalin ƙasar Portugal ne, ya taki wannan matsayi ne a karawar da ƙungiyarsu ta yi da Inter Milan a daren da ya gabata a wasan kusa da na ƙarshe na cin kofin Italiya.

Yadda al’amarin yake yanzu, Ronaldo ya ci ƙwallaye guda 763 a matsayinsa na dan ƙwallo, wanda hakan ya zarce na marigayi Josef Bican da Pele, wanda kowannensu ya ci ƙwallaye 762 a zamaninsu.

Ronaldo ya buga wa ƙungiyon ƙwallon ƙafa wasa da dama, ciki har da Manchester United da Red Devils da Real Madrid da Juventus da sauransu.

A wannan ƙarni, an tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo shi ne gaba da kowane ɗan ƙwallo a faɗin duniya wajen zira ƙwallo a raga. Sai kuma dan wasa Lionel Messi da ya yi kusa da shi da adadin ƙwallayen da ya ci guda 720.