Rubutu ne maganin ciwona, inji marubuciya Sandra Cisneros

Daga AISHA ASAS

Wasu marubuta na kallon rubutu a matsayin hanyar yin abin da zai burge mutane, ko ya wa’azantar da su, ko nishaɗantarwa, wasu kuwa na kallon baiwar rubutu a matsayin hanya ta samun kuɗi, ko samun shuhura, ko kuma sha’awa kawai.

Abin da na na ke ƙoƙarin faɗa shine, kowanne marubuci da irin fahimta da ma’anar da yake bai wa rubutunsa. Kazalika da irin rawar da yake takawa a rayuwarsa. Sai dai zai yi wuya ya tsallake waɗannan ababe da mu ka lissafo.

Sai dai a ɓangaren marubuciya Sandra Cisneros sam ba haka zancen yake ba, domin ba ta yi wa rubutu irin kallo da ma’anar da mafi rinjaye na marubuta ke yi ma sa.

A wurin Sandra Cisneros, rubutu magani ne na cutar da ke zo wa gangar jikinta, don haka ba ta ɗora shi a matsayin hanyar samun kuɗi ko nishaɗantar da al’umma, ko kuwa gyara ga wata ɓarna da ta wanzu a cikin al’umma. A wurin ta rubutun da ta ke yi ita yake amfanawa.

Kamar yadda ta ce, “wasu mutane na zuwa Coci ko wuraren samo magani idan sun samu kansu a wata matsala, don neman waraka, amma a wurina, Ina yin rubutu ne. Shi ne Cocina, shi ne maganin matsalata. Ita ce hanyar da na ke kaucewa shan magani. Kuma yana sanya min lafiyar fatar fuskata.”

A wurin wa’ansu, rubutu tamkar aiki ne na ofis, wanda wata rana kake gajiyawa da shi, amma ba za ka iya barin shi ba, saboda rufin asirin da yake kawo wa rayuwarka.

A wurin shaharariyyar marubuciyar littafin ‘House on Mango Street’, ‘Martita’ da kuma ‘I Remember You’, rubutu bai zame mata tamkar aikin ofis ba, kuma ba ta yi ma sa kallon hanyar samun dukiya da shahara, duk da cewa, wannan tunanin na ta bai hana ta cin moriyar rubutun da ta yi ba, kasancewar ta samu dukiya da kuma shuhura albarkacin littattafan da ta rubutu ta.

A wurin marubuciya Sandra Cisneros, rubutu yaƙi ne tsakanin ciwo da lafiya. Yawan rubutun da ta yi, yawan lafiyar da gangar jikinta zata mallaka.

“Na fahimci cewa, lokutan da na fi samun kaina a rashin lafiya, musamman ciwon damuwa, su ne, lokutan da na bar rubutu don in ɗan sarara. Ina yin rashin lafiya a lokacin da na bijirewa rubutu yayin da ya kusanto ni. Ina kasa samun nutsuwa a barcina.

Mafarkina kan zama marar daɗi. Duk da cewa mafi yawan mafarkai da na ke yi kan sha’anin rubutuna ne. Na jima da amincewa, mafarki saƙon gangar jiki ne zuwa ga ƙwaƙwalwa, wanda ke buƙatar kyakkyawan tunani,” in ji Sandra Cisneros.