Abinda ya kashe kasuwar littafai

Daga MUKHTAR ISA KWALISA

A wajejen shekarar 2004 littafina ya soma shiga kasuwar, na samu kasuwar littafi a wani tsari na mulkin mallaka, galibi ‘yan kasuwa ke da haƙƙin mallakar littafan da suka yi shuhura tun a waccan zamanin. Sannan manya ‘yan kasuwar littafi guda uku ne, Garba da Sauki da kuma Jakara city Bookshop duk da a lokacin su Al’amin da Hassan Miga sun soma tasowa da yunƙurin amshe ƙarfin iko. A lokacin littafi kamar gwal ne, kowanne aka buga ana siya.

Sannu a hankali, da yake duniya juyi-juyi ce sai hankalin masu karatu ya karkata zuwa ga marubutan Zariya inda suke kallon kamar su ne taurari, wanda suka gwanance wajen iya labarai masu daɗi. A haka aka ci gaba da cuɗawa sai juyin kasuwar ya ƙara karkata daga duniyar Zariya aka koma babin yaye rubutu maza inda ake cewa ai maza basa rubutu a kan rayuwar iyali da matsalar mace, sai labaran ƙarfi da tashin hankali. Amma duk wannan ciki murda da ake idan littafi ya zama na masu shagon sai da littafi ne sai su cusa abinsu su siyar.

Wannan juyin-juya-halin da aka samu kai shi ya sa wasu marubuta maza sauya salo na bada kafa, kamar Abdullahi ɗan Kantoma ya koma saka larabi wanda hakan ya sa da yawa mata suka ɗauka mace ce, sai kuma su Nazir Adam salihi suka sauya salo daga littafin tashin hankali suka koma na zamantakewa.

Wannan halin da ake ciki, sai kasuwar ta juya ga babin taƙaita siyan littafan maza ga masu zuwa siya, amma wannan sauyin bai je ko’ina ba sai littafan maza suka yunƙuro da ƙarfinsu, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Littafin Maimunatu na Ibrahim Birniwa ya zama zakaran gwajin dafi. Hakan sai ya saka su masu siyar da littafi suka shiga gwagwarmaya ganin kowanne ya tserewa sa’a. A yayin da kwararar marubuta ta yawaita, don haka kusan ko wanne lokaci akwai sabon littafi a kasuwa, wannan shi ya sa aka soma samun matsaloli nan da can game da siyar da littafi da rashin fitar da kuɗi a hannun ‘yan kasuwar.

Waɗannan matsaloli su ne guguwar da suka soma shigo da marubuta duniyar kasuwar littafi da zama publishers.

Marubuci Aminu Ala da Muhammad Lawan Barista sun soma buɗe shagon siyar da littafi, amma saboda rashin samun haɗin kai na marubutanmu na ba su kaya su zuba a shago, hakan ya sa dole suka haƙura. Ala ya ci gaba da gwagwarmaya zama mawaƙi, shi kuma Barista ya zama publisher, yana bai wa ‘Yan kasuwa su siyar su ba sa kuɗi.

Ana wannan juyi sai babbar giwar da ke jan ragamar kasuwa ta sauya salo, ta koma tura kayan da ta buga zuwa ga masu siyar da littafi na garuruwa da ke zuwa da kuɗunsu su sara su koma. Ya yi hakan ne domin hana su leƙawa shagunan sauran ƙananun ‘yan kasuwa da suke siyar da littafi.

Ta yadda kayansa ne kawai za su isa gare su. Wannan salon sai ya sa zuwan su ya ja baya. Da tafiya ta soma turawa sai ya zamana ana tura mu su kaya babu ko sisi sai sun siyar sannan su turo kuɗin.

A irin wannan lokacin su Auwalu ɗanbarno suka bar kasuwar littafi. A lokacin kuma mace mai kamar maza Sadiya Garba Yakasai ta zama kallabi tsakanin rawuna yayin da ta buɗe shagonta a tsakiyar masu kasuwancin littafi.

ƙarfi na Babbar Giwa ya sa dole aka bi salon da ya zo da shi, na tura kaya bashi sai an siyar a bada kuɗin. Don haka kasuwar littafi sai ta zama biyan bashin daddawar ƙauye.

Ana haka sai aka samu ‘yan mowa da bora, dalilin cushewar kasuwa sai ya zamana kayan basa tafiya sam, hakan ya haifar da samun littafai kashi 3: Kabewa, Cuka, Fara.

Wannan cikumurda jagwalewar kasuwa ya sa ƙungiyar HAF ta soma kafa dokar hana saka hotunan turawa da bada wani wa’adi, haka kuma aka kafa dokar tsagaita fitar da littafi na wani wa’adi, sakamakon zuwan Hukumar Tace Fina-finai da ɗab’i, sakamakon rubutun batsa da aka soma samu a wasu littafan, wannan tace littafi da aka soma sai hakan ya zama alheri, domin littafi da yake kasuwa sai da ya kusa ƙarewa.

Amma da al’amura suka kwana biyu su ka yi sanyi sai kasuwar ta ƙara cushewa haka matsaloli suka ƙara rincabewa. Wanda hakan ya haifar da koke-koke na marubuta don haka sai ƙungiyar marubuta ANA ta samar da wani kwamiti na gyaran kasuwa, wanda ba a taɓa yin kamarsa ba.

Kuma ya haɗa zakwaƙurai da idan ka gansu ka ɗauka cewar matsalar kasuwa sai dai wata kuma. Saboda a lokacin sun gama fafatawa da gwamnati da ta so share babin adabi, amma suka samu nasara akanta.

Amma ba a je ko’ina ba kwamitin Mugu Tare ya gaza, hakan ya faru sakamakon wasu marasa kishin cigaban marubuta da suka riƙa fitar da sirrin duk abinda aka tattauna suna kaiwa ‘yan kasuwa.

Mukhtar Isa Kwalisa. Matashin Marubuci kuma ɗan kasuwar littafai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *