Sin ta fitar da takardar bayani dangane da batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar a sabon zamani

Daga CMG HAUSA

Ofisoshin kula da harkokin Taiwan da na yaɗa labarai na majalisar gudanarwar ƙasar Sin, sun wallafa wata takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da dunƙulewar ƙasar Sin a sabon zamani” a yau Laraba.

An fitar da takardar ne domin jaddada Taiwan a matsayin wani ɓangare na kasar Sin, da kuma bayyana matsayin JKS da al’ummar Sinawa game da ƙudirinsu na dunkule kasar, tare da nanata matsayi da manufofin JKS da gwamnatin kasar a sabon zamani.

A cewar takardar, tun asali, Taiwan yankin ne mallakar ƙasar Sin. kuma wannan batu ne dake da ingantaccen tubali na tarihi da doka.

Haka kuma, ƙudurin babban zauren MDD mai lamba 2758, wani daftari ne da ya tanadi manufar ƙasar Sin daya tilo, wanda ƙarfin dokar dake tattare da shi, bai bayar da wata kafa ta shakku ba, kazalika, an yi ammana da shi a fadin duniya.

Bugu da kari, takardar ta ce, manufar ƙasar Sin daya tak, na wakiltar ɗaukacin matsayar ƙasa da ƙasa, kuma ta yi daidai da ƙa’idar hulɗar ƙasa da ƙasa.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa