Ƙasar Sin ta kasance ta biyu a duniya a yawan na’urorin makamashin nukiliya dake aiki da waɗanda ake ginawa

Daga CMG HAUSA

Mataimakin darektan hukumar tsaron makamashin nukiliya ta ƙasa, kana daraktan sashen sa ido kan makamashin nukiliya na ƙasar Sin, Tang Bo ya bayyana cewa, ya zuwa watan Yunin shekarar 2022, ƙasar Sin tana da rukunin tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya 54 dake aiki, baya ga tashohin samar da wutar lantarki mai aiki da makamashin nukiliya guda 23 da ake ginawa, abin da sanya ta zama ta biyu a duniya.

Tang Bo ya gabatar da wannan bayani ne, a yayin bikin buɗe taron ƙasa da ƙasa kan fasahar nukiliya karo na 29 da aka gudanar a jiya.

Ya bayyana cewa, ci gaban makamashin nukiliya, ya ba da gudummawa mai yakini, da fa’ida a fannin tabbatar da samar da makamashi, da inganta muhalli, da manufar ƙololuwar fitar da iskar Carbon mai dumama yanayin duniyarmu, da daidaita hayakin carbon.

A ƙoƙarin da take yi na bunƙasa makamashin da ake iya sabuntawa, ƙasar Sin ta ɓullo da wani tsari mai inganci, da tsaro da kuma tsari mai kyau kan makamashin nukiliya.

A halin yanzu, ana samun ingantuwar alƙaluma a tashohin nukliyar dake aiki wato ( NPPs) waɗanda ake ce suna daga cikin mafiya ci gaba a duniya.

An gudanar da taron fasahar nukiliya na ƙasa da ƙasa karo na 29 a biranen Beijing da Shenzhen daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Agusta, bisa taken “Ƙwarewar makamashin nukiliya na taimakawa daidaita iskar Carbon a nan gaba”.

Sama da ƙwararru da masana 1,200 daga ƙasashe sama da 20 ne suke halartar taron.

Fassarawar Ibrahim Yaya