Yawan injina da Ƙasar Sin ta fitar da su zuwa ƙetare a farkon rabin bana ya ƙaru da kashi 10.41

Daga CMG HAUSA

A kwanakin baya ne, ƙungiyar hadin kan masana’antun ƙera injuna ta ƙasar Sin, ta fitar da ƙididdigar dake nuna cewa, a watanni 6 na farkon bana, yawan ƙarin kuɗin da aka samu a wannan ɓangare ya ƙaru da kashi 0.7% bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da yawan kuɗin dake shafar cinikin fitar da injuna zuwa ƙetare na kasar Sin, ya kai dala biliyan 344.12, wanda ya ƙaru da kashi 10.41%.

Daga cikinsu motoci da injunan injiniya sun kasance a kan gaba.

Tun daga farkon wannan shekara, yankuna da sassa daban-daban na ƙoƙarin tinkarar mawuyacin halin da ake ciki da kuma fito da jerin matakai don daidaita ci gaba.

Mataimakin shugaban ƙungiyar Chen Bin ya bayyana cewa, duk da ƙalubalen da dama da ake fuskanta, yawan ƙaruwar da aka samu a wannan sha’ani, ya nuna tsayin daka da ci gaban kamfanonin.

A nan gaba kuma, za a gaggauta aiwatar da manufofin tabbatar da bunƙasa tattalin arziki don taimakawa kamfanoni da masana’antu wajen magance matsalolinsu.

Fassarawar Amina Xu