Tarihi ba ya mantuwa

Daga CMG HAUSA

Tun bayan fara cece-kuce game da haramtacciyar ziyarar da kakakin majalissar dokokin ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan na ƙasar Sin, masharhanta da dama ke ta bayyana mahangar su, don gane da burin Amurka na haifar da baraka ga ƙasar Sin, da lalata yanayin zaman lafiya da tsaro a zirin Taiwan.

To sai dai kuma, ga dukkanin alamu Amurka ba za ta yi nasara ba a wannan mummunar manufa, ganin cewa tuni mahukuntan Sin din suka tsara dukkanin manufofi, na dinkuwar ɗaukacin sassan ƙasar cikin lumana, ciki har da yankin na Taiwan.

Wannan manufa ce da ɗaukacin al’ummar Sinawa ke marawa baya, wadda kuma ta yi daidai da manufar farfadowar ƙasar Sin a sabon zamani.

Batun ɗinkuwar yankin Taiwan da sauran sassan ƙasar Sin, na da alaƙa da burin daukacin Sinawa tun fil azal, kuma ya dace da manufofin JKS, da gwamnatin ƙasar Sin.

Dukkanin waɗannan sassan suna nacewa manufar wanzar da zaman lafiya, da daidaito a zirin Taiwan, suna kuma daukar matakai na ingiza manufar dunƙulewar yankunan ƙasar Sin bisa doka.

A hannu guda kuma, Amurka da wasu sassan ’yan siyasar ƙasashen yamma na ta yunƙurin haifar da baraka, ta amfani da batun yankin Taiwan, musamman a shekarun baya bayan.

Kamar yadda tarihi ba zai manta da yadda Amurka ta haifar da tashe tashen hankula da yaƙe-yaƙe a sassan ƙasashen duniya daban daban ba, haka ma tarihi ba zai manta da mugun nufin Amurka na amfani da yankin Taiwan wajen haifar wa ƙasar Sin ɓaraka ba.

Bahaushe dai kan ce “Idan za ka gina ramin mugunta, to ka gina shi gajere”. Domin wata ƙila, wanda ya gina ramin shi ne zai auka a cikinsa.

Lokaci ya yi da Amurka, da masu mara mata baya a wannan mummunar aniya, za su yi karatun ta nutsu, su san cewa, duk wani yunƙuri na kawowa ƙasar Sin ɓaraka ba zai taba yin nasara ba!

Fassarawar Saminu Hassan