Rukunin sojoji injiniyoyi na tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin dake Congo Kinshasa ya kammla aikin gyara titi a ƙasar

Daga CMG HAUSA

Rukunin sojoji injiniyoyi na tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta ƙasar Sin karo na 25 dake ƙasar Congo Kinshasa, ya kammala aikin gyara titi, wanda ya ɗauki tsawon watanni 8 yana yi cikin nasara.

Yanayin damina ya lalata titin mai tsawon kilomita 96 dake tsakanin yankin Uvira da yankin Baraka na kudu maso gabashin ƙasar Congo Kinshasa, inda yake kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa da ta jama’a a yankin.

Bisa rokon sashen ba da umurni na tawagar musamman ta MƊD dake ƙasar Congo Kinshasa wato MONUSCO, rukunin sojoji injiniyoyi na tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Sin, ya fara aikin gyara titin a cikin watan Febrairun bana.

Bayan aikin da aka yi na tsawon watanni kimanin 8, sojojin ƙasar Sin sun tunkari ƙalubalen yanayi maras kyau, da cututtukan dake bazuwa a ƙasar, da kuma halin tsaron, inda suka cimma nasarar gyara titin dake tsakanin Uvira da Baraka, da kuma farfado da zirga-zirgar ababen hawa a yankin.

Fassarawar Zainab