Shawara ga Gwamna Masari

Duk da cewa ba ni cikin waɗanda ke ba gwamna shawara a hukumance. Amma a bisa ƙauna da kishi na jihar mu dai ta kanta gwamnati ta jihar mu katsina zan ƙara fatan gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ya ƙara azama wajen duba wannan lamari.

Na tabbatar da kulawar gwamna masari ga al’umma tun ya na matsayi na hudu a ƙasarmu wato kakakin majalissa ta wakilai inda a ranar 11/11/2006 mu ka haɗu a ɗaurin aure na ’yar Alhaji Rabe Abdullahi (San turakin Daura) wanda a kai a gidan Matawallen Daura.

Tun a wancen zamani na san Masari mai kula jama’a ne don haka a yau ga wata dama wacce mu ke ma ka fatan ka gama ta lafiya ka bar tarihi abin yabo ga na baya. Saƙona shi ne, Radio BBC Hausa a shirinsu mai suna gane mani hanya.

Duk wanda ya saurare su zai ji bayanai a lamarin matsalolin tsaro daga dattijo Dr Bashir Kurfi. Na san imma dai gwamna ya ji ko kuma zai samu rahoto duka dai a duba a ƙara azama ta waccen fuska. Allah ya ƙarfafe ka, Amin.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa katsina. 07066434519 \08080140820.