Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Gwamnatin Kano

Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe, wato Grassroot Care and Aid Foundation ƙarƙashin jagorancin shugaban gidauniyar Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa ta yi kira ga Gwamnatin Jihar ta Kano a kan wannan yanayi da ake ciki a wannan lokaci na damuna.

Muna kira ne ga Gwamnatin Jihar da ta duba mummunan yanayin da Jihar ke ciki na ambaliyar ruwa a kusan kowanne sassa na titunan Jihar wanda ya hada da kasuwanni har ma da unguwanni, kuma hakan na barazana da makomar Jihar tare da asarar rayuka da Kuma dukiyoyin al’umma.

Tabbas wannan yanayi ya tayar da hankula sosai duba ga ba’a taɓa samun yanayi irin wannan ba, kuma lallai idan ba’a ɗauki mataki ba nan gaba b’a san yadda lamarin zai kasance ba, akwai buƙatar Gwamnati ta yi duba na tsanakin aga yadda za a fitar da Jihar daga wannan yanayi matuƙar ana son sauke nauyin da ya rataya akan Gwamnatin.

Daga ƙarshe muna jajantawa dukkan wanda wannan al’amari ya shafa da muma ƙara kira ga ɗaukacin al’umma dasu fito su duba abinda za su iyayi iya qarfin su na samarwa da ruwan hanya a matakin kwatoci da kananan hanyoyi da suka cushe a unguwanni da kasuwanni hakan zai taimaka matuƙa.

Allah ya sa wannan shine ƙarshen fadawa cikin irin wannan yanayi duba ga zaɓe na karatowa Anan gaba kaɗan wanda da wannan zaɓe ne za a sake zaɓar wanda suka kula da damuwar al’umma da cigaban ƙasa baki ɗaya.

A ƙarshe muna addu’a Allah ya bada ikon yadda za a gyara da Kuma samun zaman lafiya a kasa baki ɗaya.

Amb Auwalu Muhd Ɗanlarabawa, Grassroot Care and Aid Foundation (GCAF), Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe.