Buba Marwa ya tallafa wa matasan Ƙaramar Hukumar Fage da kekunan ɗinki

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa, Buba Marwa ya bayar da tallafin kekunan ɗinki guda 50 da kuɗi Naira 1,000,000 don dogaro da kai ga matasan Ƙaramar Hukumar Fagge.

Tallafin wanda shugabar hukumar NDLEA mai kula da Jihar Kano da Jigawa Hajiya Maryam Sani ta miƙa a madadin shugaban a taron da aka gudanar a safiyar Alhamis a sakatariyar ƙaramar hukumar cikon alkawarin da ya yi ne ga matasan a yayin da ya kai ziyarar aiki yankin a 2019 na cewa zai bada kekunan ɗinki guda 100 da Naira 2,000,000.

Cikin alƙawarin dai ya bada kashin farko na kekuna guda 50 da Naira 1,000,000 a bara.

Wanda a wannan lokacin kuma ya cika sauran 50 da cikon kuɗin da ya alƙawarta.

A jawabinta Hajiya maryam Sani ta ce ta wakilci shugaban hukumar na NDLEA na ƙasa ne sakamakon baya ƙasar ya turo ta da cikon alƙawari da ya yi ga matasan Fagge ta ɗora su a kan sana’o’i da zai kange su daga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Shugaban ta NDLEA mai kula da Kano da Jigawa ta ja hankalin masu mulki da masu sarauta akan su riƙa gwada duk wanda za su baiwa aiki don tabbatar da ba sa ta’ammali da ƙwayoyi.

Sannan ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da masarauta da kuma ƙaramar hukumar Fagge bisa matakan da suke ɗauka na yaqi da miyagun ƙwayoyi.

Shi ma a nasa jawabin shugaban qaramar hukumar Fage, Ibrahim Muhammed Abdallah ya bayyana mutuƙar farin cikinsa bisa wannan tagomashi ya ce a lokacin da aka kawo kason farko na kekunan 50 da Naira 1,000,000 sun rabawa matasa 50 wanda jagoran Fagge tsohon kakakin majalisar Dokokin Kano Yusuf Ata ya jagoranci tatance duk waɗanda aka baiwa, wanda yanzu haka suna amfana da sana’ar ɗinki da suke.

Ya bayyana cewa Naira 1,000,000 kuma sun ajiye sai wannan karon da aka kawo cikon kekunan ɗinkin guda 50 aka yi amfani da kuxin aka ƙaro kekunan 10 suka zama 60 wanda za a raba ga matasan da dama suna cikin na farko da aka tantance guda 144.

Shehi ya ce ragowar cikon kuɗin za a sake sayo wasu kekunan don bai wa matasan da suke cikin tsarin, sannan ƙaramar hukumar za ta cigaba da bijiro da abubuwa ta ɓangarori da yawa don daqile matasa daga faɗawa shan ƙwayoyi.

Shi ma tsohon wakilin Fagge a majalisar Jihar Kano, tsohon kakakin majalisar Yusuf Abdullah Ata ya yaba da gudummuwar da shugaban na NDLEA na ƙasa ya baiwa matasan yankin da kuma yaba wa matasan bisa irin ƙoƙarin da suke na dogaro da kai da kuma nuna hali na tarbiyya.

Baturen ‘yan sanda na ƙaramar hukumar Fagge Abubakar Hamma a jawabinsa ya ce irin wannan mataki da ake ɗauka don kauda hankalin matasa daga ta’ammali da miyagun ƙwayoyi na taimaka musu wajen sauƙaƙa aikinsu ta rage masu shan ƙwayoyi suna aikata laifuka a cikin al’umma.