Wasu ƙasashen da suka daddale yarjejeniyar RCEP na fatan ƙara yin hada-hadar bada hidimomi da ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

A bana aka aiwatar da yarjejeniyar raya dangantakar abota kan haɗin gwiwar tattalin arziki a dukkan fannoni ta yanki wato RCEP a hukunce. Bisa yarjejeniyar, ƙasar Sin ta bude sabbin hukumomin samar da hidimomi 22 ga ƙasashen ƙetare, da sa ƙaimi ga hukumomi 37 da su ƙara buɗe kofa ga ƙasashen waje, waɗanda ke alamta cewa, Sin ta ƙara buɗe ƙofa ga ƙasashen waje.

Ban da haka kuma, ƙasashen da suka daddale yarjejeniyar ta RCEP da dama sun halarci bikin cinikayyar hidimomi na ƙasa da ƙasa na shekarar 2022 wato CIFTIS dake gudana a birnin Beijing, tare da shirya harkoki masu ruwa da tsaki.

Jami’ar kula da harkokin cinikayya ta ƙaramin ofishin jakadancin ƙasar Thailand dake birnin Shanghai na ƙasar Sin, Jeeranun Hirunyasumlith ta bayyana cewa, sakamakon aiwatar da yarjejeniyar RCEP, ya sa aka ƙara shigar da kayayyaki da hidimomi zuwa kasuwar ƙasar Sin, kana an sauƙaƙa ayyukan kwastam, wanda ya sa kaimi ga jigilar kaya da hidimomi tsakanin Thailand da Sin.

A nasa ɓangare, babban wakilin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya da masana’antu tsakanin ƙasa da ƙasa ta ƙasar Malaysia See Chee Kong ya bayyana cewa, an fara aiwatar da yarjejeniyar RCEP a ranar 18 ga watan Maris na bana a hukunce a ƙasarsa, kuma a watanni 7 na farkon bana, yawan kuɗin cinikayya tsakanin Malaysia da Sin ya kai dalar Amurka biliyan 114.5, wanda ya karu da kashi 20.7 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.

Ya ce ana sa ran za a kara samun ci gaban cinikayyar kaya da hidimomi tsakanin Malaysia da Sin a nan gaba.

Mai fassara: Zainab