Manoman Avocado na Kenya na cin gajiyar zurfafar dangantakar Sin da Afrika

Daga CMG HAUSA

Bayan yarjejeniyar da ƙasashen Sin da Kenya suka rattabawa hannu dangane da shigar da Avocadon Kenya zuwa kasuwar ƙasar Sin a watan Janairun bana, kashi na farko na Avocadon ya shigo cikin watan Augustan da ya gabata, kuma tuni ya fara samun karɓuwa.

Zola Franco, dan asalin ƙasar Mexico dake da dakin cin abinci a birnin Tianjin na ƙasar Sin, yanzu ya sauya Avocadon Mexico, wadda ita ce kan gaba wajen nomansa a duniya, da na ƙasar Kenya a cikin wasu girke-girkensa da suka yi fice.

Haka kuma, Avocadon manomin ƙasar Kenya Richard Tuwei, sun riga sun iso ƙasar Sin har ma an sayar da su kan farashi mai rahusa.

Richard Tuwei na ɗaya daga cikin manoma na farko da suka fara fitar da Avacado ta jirgin ruwa zuwa kasuwar ƙasar Sin.

Hukumomi a ƙasar Kenya sun ce za a riƙa kara yawan Avocadon da 100100,000 a kowacce shekara, cikin shekaru kalilan masu zuwa.

A matsayinta na ƙasa ta biyu da ke shigo da amfanin gona daga ƙasashen Afrika, yawan karuwar kayayyakin dake zuwa ƙasar Sin ya kai kaso 11.4 a shekarun baya-bayan nan.

A shekarar 2021, yawan amfanin gona daga nahiyar Afrika da ya shigo ƙasar Sin, ya ƙaru da kaso 18.2.

Fassarawar Fa’iza Mustapha