2023: Adamu ya nemi haɗin kan sarakunan gargajiya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemi goyon baya da haɗin kan sarakunan gargajiya don gudanar da babban zaɓen 2023 cikin nasara.

Adamu ya buƙaci hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu-Bashar a Fadar Abdullahi Fodio da ke Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Shugaban APCn ya ziyarci Jihar Kebbi ne don halartar ɗaurin auren ‘ya’yan Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa na APC, Alhaji Suleiman Muhammad-Argungu.

Da yake jawabi a fadar Sarkin, Adamu ya ce, “Bikin aure ne ya kawo mu Kebbi, inda muka ga dacewar mu kawo gaisuwar ban-girma gare ka a matsayinka na uba ga kowa don neman albarka da kuma neman goyon baya da haɗin kanka don gudanar da zaɓuɓɓukan 2023 cikin nasara.

“A matsayinka na uba wanda ake darajawa a cikin al’umma, wanda a kowane lokaci yake mu’amalantar talakawansa a dukkan matakai, yana da matuƙar muhimmanci a zo a nemi goyon bayanka.”

Kazalika, Adamu ya roƙi Sarkin da ya yi amfani da matsayinsa wajen nusar da matasa kan buƙatar da ke akwai na su kama kansu kafin, lokacin da kuma bayan zaɓe.