Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta soma zaman shari’a domin ladabtar da wasu manyan jami’anta kan laifuka daban-daban da ake zarginsu da aikatawa kamar rashin ɗa’a da saɓa dokokin gudanar da aiki.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jami’anta da za su fuskanci shari’a su 151 daga rassa daba- daban na faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce an soma zaman ne tun a ranar Litinin 14 ga watan Yuli, kuma za a kammala a ranar Juma’a 25 ga watan Yuli a hedikwatar ‘yan sandan da ke Abuja.
Sanarwar ta kuma ce jami’an ‘yan sanda da ake zargi da wasu laifuka da suka shafi rashin ɗa’a da karya dokokin aiki, za su bayyana ne gaban kwamitin ladabtarwa na rundunar domin fuskantar shari’a.
“Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ba za ta amince da duk wani nau’i na rashin ɗa’a ko saɓa wa doka ba, wannan tsarin ladabtarwa yana jaddada ƙudurinmu na kiyaye al’adar gaskiya da mutunta doka,” inji IGP.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, bitar ladabtarwar wani ɓangare ne na sauye-sauyen da rundunar ta ke yi da nufin dawo da amanar jama’a, da inganta ayyuka,, da kuma tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda su na bin ƙa’idojin da suka dace.
Mai Magana da yawun rundunar ya ce, kwamitin ladabtarwan wani ɓangare ne na rundunar da ke gudanar da bincike kan manyan jami’ai daga muƙamin ASP zuwa sama.
