Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, ne aka samu labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke birnin Landan na ƙasar Birtaniya.
Tsohon shugaban na mulkin sojan ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, shekaru biyu da barin mulki.
Yayin da ake ta alhini daga ciki da wajen ƙasar, mutuwarsa ta haifar da yaɗuwar labaran ƙarya a WhatsApp, Tiwita, Facebook, da sauran dandalolin sada zumunta.
Mun tattaro wasu manyan wallafe-wallafe da suka yaɗu a tsakanin ‘yan Nijeriya ta intanet.
Bayan da aka sanar da mutuwar Buhari, wani mai amfani da ɗ, Obiasogu Daɓid, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter a matsayin @afrisagacity, ya yi ikirarin cewa wannan ne karo na biyu da shugaban Nijeriya ya rasu a wani asibiti da ke wajen Nijeriya.
Ya ambaci ‘Yar’aduwa, wanda ya rasu ranar 5 ga Mayu, 2010, a matsayin shugaban ƙasa na farko, yayin da Buhari ya kasance na biyu.
Rubutun nasa, wanda ya samu masu karatu sama 100,000 kuma ya haifar da martani sama da 3000, gami da sharhi da dama, ya rubuta cewa, “Buhari ya mutu a wani asibitin Landan.” Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban Nujeriya zai mutu a wani asibiti a wajen Nijeriya. Umaru Musa ‘Yar’Adua – 5 ga Mayu, 2010. Muhammadu Buhari – Yuli 13th, 2025. Bayan shekaru 15, babu wani asibiti mai kyau a Nijeriya da wani babban mutum zai yi jinya. Abin kunya!”
Binciken gaskiya:
A wani rubutu da Garba Shehu, tsohon mai magana da yawun Buhari ya fitar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban na Nijeriya a madadin ‘yan uwa, ya tabbatar da cewa Buhari ya rasu ne a wani asibiti da ke Landan a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
Ya ce, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUUN.
“Iyalan tsohon shugaban ƙasar sun sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da yammacin yau a wani asibiti da ke birnin Landan.
Allah ya karɓi uzurin sa, Ya saka shi a Aljannatul Firdaus, Amin,” inji sanarwar.
Shugaban Nujeriya na yanzu, Bola Ahmed Tinubu ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar kan rasuwar Buhari.
“A cikin tsananin baƙin ciki da bakin ciki ne na samu labarin rasuwar, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), GCFR, wanda na karɓi mulki a hannun sa, wanda ya rasu yau Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti a ƙasar Ingila.
“Shugaba Buhari ya kasance mai kishin ƙasa, soja,” inji shi.
A halin da ake ciki kuma, wani bincike da Google ya bayyana ya nuna cewa Umaru Musa Yar’adua wanda ya mulki Nijeriya tsakanin shekarar 2007 zuwa 2010, ya rasu ne a ranar 5 ga watan Mayun 2010 a fadar shugaban ƙasa ta ɓilla.
Shi ne Shugaban Nijeriya na biyu da ya rasu a Aso Rock ɓilla bayan Janar Abacha.
Duk da yake gaskiya ne Buhari ya rasu a asibitin Landan, ɗaya daga cikin manyan asibitoci masu zaman kansu a ƙasar Birtaniya, amma maganar cewa Yar’adua ya mutu a wajen Nijeriya aarya ce kuma yaudara ce.
Haka zalika, wani shahararren masoyin Buhari (Mai goyon bayan Buhari) kan dandalin Tiwita, Imran Muhammad, a yayin zaman makokin Buhari, ya wallafa cewa ɗan uwansa, Mamman Daura, na jinya a wani asibiti a ƙasar Birtaniya, inda ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya.
Ikirarin wanda ya samu sama da masu kallo dubu 200 da kuma kusan martani dubu 4, ya ce: “Tunanina na tare da Mamman Daura, ɗan uwan marigayi Shugaba Buhari, wanda aka ce yana jinya a wani asibiti a ƙasar Birtaniya, ina yi masa addu’ar samun lafiya, da kuma ta’aziyya ga iyalansa a wannan mawuyacin lokaci.
Irin wannan saƙon da @ManLikeIcey ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce: “Yayan Buhari, Maman Daura, shi ma yana cikin wani mawuyacin hali a wani asibiti a Birtaniya.”
Mamman Daura dai na kusa da Buhari ne kuma ana yi masa kallon ɗaya daga cikin jiga-jigan a hannun daman Buharin da mutane da dama ciki har da uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari a lokacin suka yi imanin cewa ya na da tasiri a wurin Buhari.
GASKIYA: Hotuna sun fito a yammacin ranar Litinin, 14 ga watan Yuli, 2025, da ke nuna Mamman Daura mai shekaru 85 a duniya yana karɓar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya ziyarci iyalan Buhari a birnin Landan domin ta’aziyya.
ɗaya daga cikin hotunan da Tolu Ogunlesi, mataimaki na musamman kan sabbin kafafen sadarwa na zamani a gwamnatin Buhari ya yaɗa, an gan shi tsaye yana musabaha da mataimakin shugaban ƙasar.
Da yake yaɗa hotunan, ya ce, “Ziyarar ta’aziyya: HEɓP @officialSKSM tare da Mamman Daura, London, UK.
Maganar cewa Mamman Daura na jinya a wani asibiti a Landan ba gaskiya ba ne.
Wani mummunan labari da aka yaɗa a shafukan sada zumunta a lokacin rasuwar Buhari shi ne cewa gawarsa ta iso Nujeriya a ranar Litinin bayan an dawo da shi daga Landan.
Gidan Talabijin na Eaglet, a wani saƙo da ya wallafa a Facebook, ya ce, “Rawar Tsohon Shugaban ƙasa Buhari Ya Isa Nijeriya.
“Gawar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ta iso Nijeriya a yau 14 ga watan Yuli, 2025 daga Landan, tare da rakiyar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.
Bidiyon da gidan Talabijin na Eaglet Tɓ ya maƙala a shafinsa, wani Tijay Bala mai mabiya 85,000 ne ya wallafa a Facebook.
A ranar Litinin 14 ga watan Yuli ne gwamnan jihar Katsina Dikko Radda a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa za a yi jana’izar marigayi tsohon shugaban aasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke Daura a ƙaramar hukumar Daura a ranar Talata 15 ga watan Yuli 2025.
Bidiyon da ke cewa gawar Buhari ta iso Nijeriya ne a ranar Litinin din da ta gabata kafin gwamnan ya yi magana ko Shettima (wanda ya kamata ya dawo da gawar Buhari gida) ya ziyarci iyalan a Landan.
Jirgin da ke cikin faifan bidiyon, wanda 5N-FGT za a iya gani a kai, shi ne Boeing Business Jet 737-700, wanda a baya NAF-001 ya keɓanta, wanda ya yi aiki a matsayin jirgin shugaban Nujeriya na farko daga 2005 har zuwa lokacin da aka maye gurbinsa a 2024 tare da sabon Airbus A330.
Maganar cewa gawar Buhari ta iso Nijeriya ƙarya ce, kuma bidiyon tsoho ne saboda laƙabin jirgin 5N-FGT, wanda yanzu ba shi ne jirgin shugaban ƙasa a Nijeriya ba.
Wannan yana nuna yadda bayanan ƙarya ke yazuwa cikin sauƙi yayin faruwar manyan mabubuwa.
