Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi sabon Kwamishina

Daga RABIU SANUSI, a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda yayin da ya rage kwanaki kaɗan kafin babban zaɓen 2023.

Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya raba wa manema labarai ranar Talata.

Kamar yadda sanarwar take cewa, an sauya wa CP Mamman Dauda wurin aiki zuwa Jihar Filato, sannan an maye gurbinsa da sabon CP Muhammad Yakubu domin ɗorawa daga inda ya tsaya.

Sanarwar ta ce CP Ita Lazarus Uko-Udon ya dawo Kano a matsayin Mai kula da shiyyar Kano ta tsakkiya, sauran sun haɗa da DCP Adamu Isa Ngoji da DCP Abdulkadir El-Jamal da za su kasance masu kula da shiyyar Kano ta Kudu, Wanda DCP Abaniwonda S.Olufemi a matsayin mai kula da shiyyar Kano ta Arewa yayin gudanar da aikin zaɓe.

Daga bisani sanarwar ta nuna matuƙar godiya ga al’ummar Jihar Kano bisa goyon bayan da suke ba wannan rundunar yayin gudanar da aikinta.

Rundunar ta ƙara bayyana neman haɗin kan jama’a bisa dukkan wasu abubuwan da zai kawo cigaba musamman wajen nunan goyon bayan samun tsaro da kare haƙƙoƙin al’umma a jihar.