Yadda cinikin bayi ya shafi Arewacin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Cinikin bayi wani lamari ne mai ɗumbin tarihi wanda ya samo asali shekaru aru-aru.

A duk lokacin da baƙar fata suka tuna da yanayin da kaka da kakanninsu suka shiga a zamanin cinikin bayi, akasarin su suna fuskantar ɓacin rai.

An shafe sama da shekaru 400 ana gudanar da cinikin bayi inda akasarin bayin ana ɗibarsu ne daga nahiyar Afrika a tafi da su sauran nahiyoyi musamman yankin Amurka da Turai.

Nijeriya na daga cikin ƙasashen yammacin Afrika da ke da guraren da aka mayar cibiyoyin hada-hadar bayi kamar Badagry da ke wajen birnin Legas a wancan lokaci.

Ƙasashen Sifaniya da Portugal da Birtaniya da kuma Faransa ne dai kan gaba a wannan harka ta cinikin bayi.

Duk da cewa babu wata sahihiyar ƙididdiga da za ta nuna adadin bayin da aka kwasa daga nahiyar Afrika zuwa sauran ƙasashe, sai dai an yi ƙiyasin cewa an kwashi sama da mutum miliyan 12 a tsawon shekarun da aka ɗauka ana cinikin bayin.

Saboda muhimmancin wannan lamari ne ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware duk ranar 23 ga watan Agustan kowacce shekara domin yin waiwaye kan wannan batu.

Dakta Babangida Jibril, wani masanin tarihi da ke koyarwa a kwalejin horar da sojoji ta NDA da ke Kaduna, ya bayyana irin yadda cinikin bayi ya yi ga ci gaban arewacin Nijeriya da kuma nahiyar Afrika.

A cewarsa, a lokacin da Turawa suka je Afrika, sun yi amfani da wata hikima da ake kira ‘trans-atlantic slave trade’, wato wani nau’i ne na cinikin bayi da Turawan ke yi inda suke zuwa Afrika su sayi bayi, sai su ɗauke su cikin jirgin ruwa su kai su yankin Amurka, daga can idan suka yi noman rake, za a ɗauki sukarin da aka yi da raken zuwa nahiyar Turai.

Sai su yi amfani da kuɗin da suka samu daga sukarin da suka sayar kuma sai su sake dawowa Afrika su sayi wasu bayin.

Ya ce, cinikin bayi ya shafi arewacin Nijeriya da nahiyar Afrika gaba ɗaya, inda ya ce, a lokacin ana yawan yaƙe-yaƙe tsakanin garuruwan da ke arewacin Nijeriya, idan aka kama bayi, akwai dillalai da suke ɗaukan bayin, za su kai su har bakin Kogin Atlantic, inda daga nan kuma ake ɗaukar su domin tafiya Amurka.

“Shekarun da aka ɗauka ana cinikin bayi a nahiyar Afrika na daga cikin abin da ya sa nahiyar ta zama koma baya wajen ci gaban tatalin arziki da na ilimi da ƙere-ƙere,” in ji Dakta Babangida.

“Lokacin da nahiyar Turai ta ƙara samun ci gaba na ilimi sai ya zamana wani yanayi na tattalin arziki ya shigo wanda ake ce wa Industrial Revolution, wanda wani yanayi ne na amfani da kayan ƙere-ƙere, wanda wannan ya ja ‘yan kasuwa na nahiyar Turai ya zamana ba su buƙatar bayi, hakan ya sa aka bar cinikin bayi,” in ji shi.

Masana na ganin cewa bayin da aka kwasa zuwa nahiyar Turai da Amurka, an yi amfani da su wurin gina tattalin arzikin nahiyoyin, inda akasari bayin na aiki tun daga safe har dare a gonaki da masana’antu.

Ruɗun da aka shiga a nahiyar Afrika a lokacin, ya hana jama’ar yankin natsuwa su yi tunanin ci gaban kansu sakamakon fargaba da ake ciki a kullum.

Bugu da ƙari kuma matasa majiya ƙarfi da ya kamata a ce sun tsaya nahiyar ta Afrika an more su, su ne aka rinƙa kwashewa zuwa sauran ƙasashe domin aikin bauta.

Yanayin rayuwar Bayi:

Kamar yadda ya tabbata a tarihi, yanayin kamen bayi a zamanin Cinikin Bayi na Atalantika ya kasance mai muni da tsanani kwarai da gaske fiye da sauran cinikayyar bayi da aka yi a sauran sassan duniya. Domin kuwa, mafiya yawa daga cikin masana tarihi sun tabbatar da cewa rayuwar bayi a wannan zamani musamman bayin da su ke noma a gonaki ta kasance ta wahala da kuma keta haƙƙin ɗan adam. Saboda ya tabbata cewa mafi yawancin bayin ana mu’amalantar su ne kamar dabbobi. Kuma haka ta faru ne sakamakon rashin imanin Turawa saboda suna ganin shi bawa ba shi da wani ‘yanci tun da sayen sa aka yi.

A nahiyar Amurka kuwa da ake kai bayin daga Afirka, ana tilastawa bayin su yi noma a manyan gonaki na tsawon lokutai da suka wuce kima. Duk bawan da kuma ya ƙi yi ko kuma bai yi yadda ya kamata ba, to ana hukunta shi kamar dabba. Misalin hukuncin shine, akan yi musu bulala da ta wuce kima har sai jikin su ya fashe, ko a yanki naman jikin su, ko kuma a hana su abinci a wannan rana.