Me ya ɗimauta El-Rufa’i?

Daga Muhammad Bello Sharaɗa

Nasir El Rufai ya fada wa BBC lokaci zai yi cewa zai bayyana sunayen ƙarara na mutanen da suke yi wa Buhari maƙarƙashiya kuma suke ba shi muguwar shawara. Kuma ya ce zai bayyana waɗanda basa son Tinubu ya yi nasara.

A kwanan nan kuma El-Rufa’i ya gaya wa jama’a kowa ya ɓoye takardar nairori da yake da ita, da zarar Sanata Uba Sani ya zama gwamnan jihar Kaduna za su tsaya da shi da Tinubu su dawo wa da kowa kuɗinsa, babu kuɗin kowa da za su yi ciwon kai.

El Rufai fa da shi da ɗansa da wasu gwamnoni, sun shiga ruɗu, suna ta sambatu. Hankalinsu ya tashi, su shiga nan su fita can, saboda zaɓe saura kwanaki kaɗan kuma ba nasara suke hangowa ba illa faɗuwa.

Mu ɗan koma baya a tarihi.

A shekara biyu da ta gabata, na yi rubutu a kan waɗanda a fahimtata su ne masu faɗa-a-ji a gwamnatin Buhari ta APC. Na bayyana sunayensu ƙarara. Waɗannan mutanen a gurina, su ne; Alhaji Mamman Daura da Alhaji Sani Zangon Daura, su biyun suna cikin dattijai na Arewa da ake kiransu da Kaduna Mafia. Wadannan mutanen basu riƙe da kowanne muƙami a yanzu. Kafin rasuwar Abba Kyari da Ismail Isa Funtua suna cikin wannan lissafin.

Bayan su akwai Ambasada Kazaure, Shugaban tsare-tsare na PMB da Sabi’u Tunde ɗan ƙaramin sauro na fadar Aso Rock kuma Keɓantaccen Sakatare na Buhari da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Gidi Mustapha da Antoni Janar Abubakar Malami da shugaban ma’aikata Farfesa Ibrahim Gambari da Janar Yusuf Burutai, jakadan Najeriya a ƙasar Benin da Aisha Buhari da Yusuf Bichi Darakta na DSS da Janar Munguno mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkar tsaro NSA da Ahmed Rufai darakta na NIA.

A cikin waɗanda suke kewaye da Buhari a gwamnoni kuma suke juya lamura akwai Nasiru El Rufai da Atiku Bagudu da Badaru Abubakar. Waɗannan mutanen sune hakikanin CABALS. El-Rufa’i yana cikinsu, kuma yana sane yake wannan zage-zagen. Dabara ce da makirci, shi ya sa na ce, ƙwaro ne.

Me ya sa na ce haka?

El-Rufa’i ya yi wa manyan Arewa tatas. Ya kira su zatcizai. Ya kira su dattijan banza. Ya kira su dattijai marasa daraja. Gwamnan jihar Kaduna ya harzuƙa matuƙar gaske. Wancan satin Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya keta gwamnan babban banki Godwin Emefile da shugaban qasa Muhammad Buhari da harshen Yarbanci. Shi kuma El-Rufa’i nasa cin fuskar da Hausa ya yi. Da El-Rufa’i da Tinubu sun shiga damuwa ne sosai a kan abubuwa guda biyu: Na farko, rashin man fetur da tsadar sa. Na biyu, ƙarancin sabbin kuɗi da aka canza musu kala.

Babban abin da ya tashi hankalin El-Rufa’i da Tinubu shi ne, tunanin saura kwanaki ƙalilan a buga zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dattijai da tarayya. Rashin tsabar kuɗi da man fetur a hannun mutane da makamashin ababen hawa da injina. A lissafin El-Rufa’i da Tinubu, idan an yi zave a wannan yanayin jam’iyyar APC za ta faɗi warwas. Idan a wannan halin aka kaɗa ƙuri’a, jama’ar ƙasa za su huce a kan APC su kayar da ita. Su kuma tashin hankalinsu shi ne rasa gwamnati.

A lissafin El-Rufa’i, Bola Ahmed Tinubu zai faɗi zaɓe kuma Atiku Abubakar zai yi nasara. Da BAT da AA don sun ci ko sun faɗi, shi ba shi da asara, saboda haƙiƙar ɗan takararsa shi ne Rotimi Ameachi amma kuma bai samu ba.

Hikimar El-Rufa’i ita ce, idan ya riqa banbami da hayaniya mutanen Kudu da ‘yan jam’iyyar APC za su kalle shi a matsayin mai ƙoƙari kuma ɗan amana, kuma a siyasance ya cika alkawarinsa, don haka da zarar APC ta faɗi, shi ne zai yi uwa da makarɓiya a wajen rarrashin Inyamurai da Yarbawa da rowonsu su karɓi ƙaddarar zaɓe domin Najeriya ta zauna lafiya kuma su shiga ƙulle-ƙullen karɓe jam’iyyar APC ta dawo hannunsu.

Duk wannan sambatun da ɗimautar ta gangan ce. Sun san za a faɗi. Al’ada ce ta El-Rufa’i ya ƙirƙiro zance da babu shi kuma ya kafe a kansa, har mutane su ɗauke shi gaske, amma giri ne. Shi da kansa ya faɗi haka a littafin Olusegun Adeniyi da kuma Accidental Public Servant nasa, da shaidar da Obasanjo ya yi masa a littafin MY WATCH da kuma yadda Nuhu Ribadu ya nuna bacin rai da abin da El-Rufa’i ya faɗa a kansa a littafin, ya kuma ce zai rubuta nasa don goge sharri da wage da El-Rufa’i ya yi masa. El-Rufai ba domin talaka yake magana ba. Kada wanda ya gaskata zancensa.

Bello Muhammad Sharaɗa ɗan ƙasa ne mai bayyaba ra’ayi. Ya rubuto daga Kano Nijeriya.