Lokacin farkawar Arewa ya yi!

Daga ZAINAB AHMAD BINT HIJAZI

Sau da yawa, nakan zauna na yi wa kaina wasu tambayoyi masu ɗaure kai kamar haka: Anya da gaske muke idan muka ce muna son gyara ƙasar nan kuwa?

Anya mu ‘yan Arewa mun san ciwon kanmu kuwa? Yaushe za mu yi wa kanmu faɗa a kan abin da ya dace da mu da wanda bai dace da mu ba?

Yaushe za mu daina zama kamar mayunwatan kaji masu jiran a watsa musu tsabar su tsattsaga? Ba mu ganin yadda al’ummomin wasu yankunan na Nijeriya suke yi ne?

Waɗannan tambayoyin sun ƙara ƙaimi a zuciyata sakamakon abubuwan da na ga suna wakana a cikin ‘yan kwanakin nan da babban zaɓen 2023 ya gabato. Na firgita matuƙa ganin yadda mutanenmu ke rawar ƙafa gurin bin mutanen da suka jefa mu cikin wahala a ƙasar nan, suna so su ƙara ba su ragamar mulkin da za su ci gaba da yin sukuwa son ran su.

Na yi mamakin yadda mutanenmu suka manta da uƙubar da muka sha tsawon shekaru bakwai, kuma muke ciki har zuwa yau, suke bibiyar wanda yake gaya mana zai ɗora daga inda aka tsaya. Manufa, wahalar da ake sha ita ce za a ci gaba da sha a wasu shekaru huɗu masu zuwa, ko ma fiye.

Na yi mamakin yadda kuɗi suka sa mutane suka kau da kai daga gaskiya zuwa kasuwar buƙatar ransu. A yau, sai ka ga wanda ba ka zato ya yi zarya ya bi layin da ya san ba zai ɓulle ba, ba don komai ba sai don an ce ya zo a tafi tare da shi. Da ma an riga an tsiyata mutanen Arewa, kowa na neman inda zai samu abin miya.

To amma shin ashe har yunwar tamu ta kai yadda duk mutunci da aƙidar mutum za a iya sayen sa ya aikata ba dai-dai ba don wata ƙaramar buƙatar shi? Shin mutum ya manta da cewa wannan buƙatar tasa da zai biya sakamakon ta shi ne faɗawar sauran miliyoyin jama’a cikin tarkon ƙaƙa-ni-ka-yi? Ashe masifun da muke ciki ba darasi ba ne na mu haɗa kanmu don fita daga ƙangi?

Ashe duk kuka da ihun da muka yi a kan zaluncin da aka yi mana a baya bai ishe mu darasi ba? Ashe ƙarya muke yi lokacin da muka fito da sunan masu kishin Arewa da nema mata sauƙi?

Me ya sa ɗan Arewa yake da sauran mantuwa? Shin ciwon mantuwa ke damunmu, irin wanda aka ce yana damun ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun da ke kan gaba wajen neman mulki? Idan ‘yan Arewa sun manta, bari in ɗan yi musu tuni.

A cikin shekarun nan bakwai, mutum dubu nawa ‘yan ta’adda suka bi har ƙauyukansu suka yi musu kisan gilla? Kun manta da yadda ake shanya gawarwaki a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna bayan harin ta’addanci? Sau nawa aka shiga ƙauyuka aka buɗe wuta, wani sa’an ma a cikin masallaci, ko a kasuwa, aka bindige ɗimbin bayin Allah? Mun manta?

A da, komai dare za ka iya ɗaukar mota ka kama hanyar Kaduna daga Abuja, ko daga Sokoto zuwa Gusau, ko Katsina zuwa Zariya, ko Kano zuwa Kaduna, ko Gombe zuwa Jos, ko Makurdi zuwa Abuja. A yau fa? Da rana tsaka ma cikin tsoro muke bin waɗannan hanyoyin. Muna tsoron ‘yan kidinafin da sauran ‘yan tarzoma. To ina ajandar da tallata mana a 2015 cewar idan an ci zaɓe za a magance matsalolin tsaro?

Na biyu an ce za a magance matsalolin tattalin arziki idan an ci zaɓe. Shin an cika? Wane irin bala’in fatara da yunwa ne ba mu gani a yau? Farashin kayan masarufi ya ninninka daga 2015 zuwa yau. A shekarar 2015 ana sayen buhun shinkafa a dubu takwas da ɗoriya, a yau shinkafa ta koma dubu arba’in da ‘yan kai. A 2015 fetur na tsakanin N87 zuwa N97, a yau ana litar fetur ta koma N345.

Cin abinci yana neman ya gagari jama’a. Babu aikin yi ga matasa. Masana’antu sun durƙushe. Yanzu haka muna cikin ibtila’in ƙarancin naira tun daga lokacin da CBN ya ƙaƙaba wa ƙasar nan tsarin shirme na sauyin kalar naira. Yau mun wayi gari mutum da kuɗin sa an mai da shi maroƙi don son zuciya da rashin tausayin wasu ‘yan tsiraru. Nijeriya ba ta taɓa ganin bala’i irin wannan ba tun daga 1984!

Idan ku ka lura, talaka bai taɓa shiga matsi irin na wannan zamanin ba, aƙalla dai tun daga wanda ya sha a 1984. Babu tsaro, babu lafiya, babu abinci, ba wuta, ba ruwa, ba lantarki; ba ta inda talaka ke samun sauƙi.

Dubi hanyoyin Arewa. Dubi makarantun Arewa. Dubi mutanen Arewa. Duk inda ka zagaya, ba abin da za ka gani sai fatara da yunwa da rashin aiki yi na matasa, ga almajirai nan kamar farin ɗango, ga asibitoci babu magani; babu, babu ta yi mana yawa!

Na uku, an ce za a yi yaƙi da cin hanci da rashawa. To wa aka yaƙa? Wa aka kama? Wa aka hukunta? Duk wani wanda ake yi wa kallon ɓarawo a zamanin Jonathan, a yau waliyyi ne. Da su ake damawa. “Masu gudu” ba su gudu ba! Ka duba, wasu ƙasurguman maciya hanci da rashawa ma da kotu ta tura gidan yari, tuni aka ce an yafe musu, an fito da su, domin su taimaka a ci zaɓe!

Sakin waɗannan ƙasurguman maciya hancin daga gidan gyara hali ya karya lagon yaƙi da cin hanci, ya sa an ɗauki batun yaƙi da cin hanci da rashawa a matsayin wani wasan yara ko dirama. A yau, ba wanda za ka gaya wa ana wannan yaƙin tsakani da Allah ya ɗauke ka da daraja ko mai cikakken hankali.

Duk wani babban alƙawari da aka ɗauka kafin zaɓen 2015, an kasa cika shi. A madadin hakan ma, an mayar da ƙasa baya. An samu cigaban mai ginar rijiya. To wai a hakan ne har wasu ke cewa wai Arewa ta yi mubaya’a, ta amince da yekuwar “sake ɗorawa a inda aka tsaya”.

Shin kai ɗan Arewa nawa aka ba ka da ya isa har ya sa ka kawar da kai daga gaskiya? Me ku ke nema a duniya da ku ke sayar da mutunci da ‘yancinku da na yankin ku don cimma wannan buƙata? Shin kuna ma tuna Allah zai iya ɗaukar rayuwar mutum ba tare da ya shirya ba?

A lokacin da kuke kokawar jefa mutane a wata masifar, shin kun zauna kun yi nazari a kan mutanen da ke hannun ‘yan bindiga da waɗanda aka mayar marayu da waɗanda ke zaune a dandalin gudun hijara don rashin kulawa, da ma waɗanda aka aika da su barzahu? Kenan kun yarda kun amince a ci gaba da abubuwan da ke faruwa na rashin gaskiya a ƙasar nan?

‘Yan Arewa ku aje son zuciya a gefe, ku natsu, ku nema wa kan ku mafita. Kar ku yarda a sake rufta ku ramin da fitowar ka sai Allah. Shawara ce.

Wallahi idan ba mu shiga hankalin mu ba, to tabbas za mu faɗa wahalar da ta fi wadda muke ciki a yanzu. Mu yi tunani a natse, shin abin da za a ba mu zai yanke mana talauci ko ya ishe mu tsawon shekaru huɗu zuwa takwas? Shin mecece makomar mutanen mu na karkara waɗanda ba su da hanyar abinci sai sun juya ‘yan kuɗaɗen hannun su ta hanyar kasuwanci?

Mutanen da ƙauyukan su ba su da banki balle su san wani abu wai shi ATM, mutanen da ba su da wayoyin da za su iya sauke manhajar da za su koma kashles. Mutanen da suka saba ba ni gishiri in ba ka manda. Mutanen da ba su ma da ilmin zamani bare sanin yadda ake hawa intanet. Kar kuma mu manta da kuɗaɗe daban-daban da ake kwashe wa mutane da sunan harajin ajiya a banki.

Wato ta ko’ina ba a so talaka ya samu sauƙi. Kar mu manta bayin Allah da ke daji don gazawar gwamnati da babun da ta hana ‘yan’uwan su karɓo su. Kar mu manta waɗanda aka kashe don rashin kuɗin fansa. Mu koma manoman da aka hana noma don tsoron ‘yan ta’adda da barazanar sace su da cin zarafinsu.

Idan muka lura, duk wata hanyar samun sauƙi an toshe wa talaka. Mutane na zaune cikin uƙuba da rashin makama. A kuma haka ake son sake tura mu masifar da ta fi wannan. Mu sake nazari, mu fara gyara kawunan mu da zuciyoyin mu, sai Allah ya taimake mu.

Kafin ka jefa ƙuri’a, don girman Allah ka yi tunani da dogon nazari, ka aje son zuciya a gefe, ka dubi daga inda aka taho, da inda ake yanzu, ka yi wa kan ka adalci, ka yi wa talakawa da mabuƙata adalci ka zavi wanda ka amince zai ƙoƙarta kawo sauƙi gare ka da ma ƙasar gaba ɗaya. Shawara ce. Kamar yadda marigayi Sa’adu Zungur ya faɗa:

“Mu dai burin mu gaya muku,
Ko ku karɓa ko ku yi dariya.

“Dariyarku ta zam kuka gaba,

Da nadamar mai ƙin gaskiya!”

Hajiya Zainab Ahmad Bint Hijazi mai sharhi ce kan al’amurran yau da kullum.