Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta gargaɗi mutane kan ƙauracewa tashin-tashina – Rikicin Masarauta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da babbar kotun tarayya da ke Kano ke yin hukunci kan wasu al’amura da suka shafi Masarautar Jihar a yau, rundunar ‘Yan sandan Jihar ta yi kira ga al’umma da su gujewa dukkan abun da zai janyo rikici ko hayaniya a dukkan sassan Jihar.

Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya faɗi haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis inda ya ce haƙƙin hukumarsu ne su kula da rayuka da dokiyoyin al’ummar Jihar, dan haka kar su amincewa duk wani yunƙuri na tada-zaune-tsaye a lokacin gudanar da shari’ar ko bayan haka.

A ƙoƙarinta na hana ɓarna ta dukkan hanyoyin da suka dace, rundunar ta gargaɗi mutane da su kiyaye abubuwa kamar haka:

Na farko, Rundunar tare da sauran hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar, sun dakatar da zanga-zanga tare da nau’in taro mai alaƙa da hakan, dan haka jama’a su kiyaye. Sannan duk wanda aka kama da hanu cikin aikata hakan, to doka za ta yi aiki a kansa.

Na biyu, za’a sanya jami’ai a wurare da dama, saboda haka ake so al’umma ta basu haɗin kai ta yadda za su ke sanar da su duk wani bayani mai muhimmancin da aka san zai taimaka wajen tabbatar da tsaro.

Na uku, hukumar ta buƙaci tawagar ƴan banga da mafarauta da makamantansu da su ƙauracewa shiga cikin harkar tsaron a kowane yanki na Jihar.

Daga ƙarshe, rundunar ta ce, za’a iya neman su ta kafofin Facebook, Twitter, Instagram, da TikTok a adireshin ‘Kano State Police Command’ da kuma ‘NPF Rescue Me’ a manhajar ‘Play Store’, ko kuma ta lambobi kamar haka; 08032419754, 08123821575 09029292926