Sallamar Kanu aka yi ba wanke shi ba – Malami

Spread the love

Ofishin Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, ya ce sake Nnamdi Kanu da aka yi ba wanke shi aka yi ba an sallame shi ne kawai.

Ofishin ya yi wannan ƙarin hasken ne don kawar da sahakku a tsakanin ‘yan ƙasa kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ɗauka dangane da shari’ar Nnamdi Kanu.

Hadimin Ministan Shari’a, Dakta Umar Jibrilu Gwandu ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Alhamis.

Ya ce, jama’a su sani sallama kawai kotun ta yi wa Kanu amma ba wanke shi ba, domin kuwa shari’a ba ta ƙare ba.

Kazalika, ofishin ya ce za a duba sauran batutuwan da ke gaban hukumomi da suka shafi Kanu kana daga bisani a a sanar da jama’a yadda ya kamata.

By Editor